Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta samu wani mutum mai shekara 55, John Nwawuto Anoruo, da laifin yin ƙaryar cewa shi lauya ne da kuma amfani da hatimin bogi na ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), inda ta yanke masa hukuncin tara.
Mai shari’a A.M. Lawal ya yanke hukuncin ne bayan Anoruo ya amsa laifuka biyu da suka haɗa da amfani da hatimin NBA na bogi da kuma yin ƙarya cewa shi ƙwararren lauya ne.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama Anoruo a ranar 20 ga Afrilu, 2026. Bincike ya nuna cewa yana gudanar da cibiyar ba da shawarwari kan harkokin shari’a da ilimi a yankin Ikorodu na Legas, duk da cewa bai cancanci aikin lauya ba.
Lamarin ya fara ne bayan ya shigar da ƙorafi ga EFCC a madadin wasu kwastomomi, amma binciken hukumar ya gano cewa takardun sun ɗauki hatimin NBA na bogi. Anoruo ya amsa cewa ya samo hatimin ne daga wani wurin kasuwanci a Legas.
Ya kuma shaida wa masu bincike cewa ya yi karatun digirin shari’a a Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka, amma bai taɓa halartar Makarantar Horar da Lauyoyi ta Nijeriya (Nigerian Law School) ba, wanda ya sa bai cancanci aikin lauya ba.
Shaidar jami’in binciken EFCC, Umar Faruk Ahmad, ta nuna cewa Anoruo ya karɓi Naira miliyan 7.5 daga wani aikin shari’a, amma ya bai wa wani ƙwararren lauya Naira miliyan 1.5 domin ya gudanar da shari’ar a madadinsa.
Jami’in ya ƙara da cewa lokacin da Anoruo ya amsa gayyatar EFCC, ya isa ofishin hukumar sanye da kayan aikin lauya. Binciken da aka yi a gidansa ya kai ga gano hatimin NBA na bogi mai lambar rajistar wani lauya daban.
Bayan Anoruo ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su, kotu ta ci shi tarar Naira 120,000 kan laifi na farko da Naira 150,000 kan na biyu, jimillar Naira 270,000.
Kotun ta kuma ba da umarnin a ƙwace rigar lauya da hatimin NBA na bogi da aka samu a hannunsa tare da miƙa su ga gwamnatin tarayya ta hannun EFCC.
.
