Fulani makiyaya sun zargi hukumar OYRLEA da ƙwace dabbobinsu ba bisa ƙa’ida ba a Oyo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fulani Makiyaya da ke ƙaramar Hukumar Ido a Jihar Oyo sun zargi jami’an Hukumar Tabbatar da Bin Doka ta Jihar Oyo (OYRLEA) da karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, nuna wariya da kuma ƙwace dabbobinsu ba tare da hujja ba.

Makiyayan sun yi waɗannan zarge-zarge ne a ranar Asabar yayin da suka kai wasu ‘yan jarida zagayen wuraren da suka ce jami’an hukumar suka ƙwace musu dabbobi.

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a yankin, Alhaji Ahmed Babangida, ya yi zargin cewa jami’an OYRLEA ne tare da jami’an Amotekun Corps da masu tsaron sa-kai suka gudanar da waɗannan samame.

A cewarsa, an kwace shanu 10 a ƙauyen Goronjo, sannan daga baya hukumar ta sayar da su ba tare da izinin mai su ba.

Ya kuma yi zargin cewa an saki shanu 16 mallakar Abubakar Mohammed na ƙauyen Konguo ne kawai bayan ya biya kuɗi har Naira miliyan 8.5.

Babangida ya ƙara da cewa, an kuma kwace wasu shanu tara a Sonso, yayin da har yanzu ba a mayar da wasu shanu 10 da tumaki biyar da aka ƙwace a wasu wurare daban-daban ba.

Ya bayyana cewa waɗannan matakan sun jefa makiyayan cikin babbar asarar tattalin arziki tare da ƙara tsananta musu matsin rayuwa.

A cewarsa, duk da kuɗaɗen da aka ce an karɓa daga wasu daga cikin makiyayan, dalilan da jami’an hukumar suka bayar na ƙwace dabbobin ba su da tushe.

Shi ma wani makiyayi, Alhaji Abubakar Saliu, ya zargi jami’an da gudanar da mafi yawan samamen ne cikin dare, yana mai cewa sun riƙa bayyana cewa suna aiki ne da umarnin Gwamnatin Jihar Oyo.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Hukumar Tabbatar da Bin Doka ta Jihar Oyo (OYRLEA) ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan waɗannan zarge-zargen ba.

By ukarofi