Hukumar alhazan Kano za ta rufe karɓar kuɗin Hajjin 2027 a 25 ga Agusta yayin da ta ƙayyade farashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa Naira miliyan 7 ne ƙayyadadden farashin aikin Hajjin 2027 ga maniyyata dafa sassan jihar.

Darakta-Janar na hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle ne ya sanar da haka a wata takarda, ranar Talata.

A cewar hukumar, 25 ga watan Agusta, 2026 na nan a matsayin ranar ƙarshe ta biyan kuɗin rajistar Hajjin na 2027.

“Baki ɗaya waɗanda ba su miƙa fasfo ɗinsu na ƙasa-da-ƙasa ba, su yi hakan kafin wa’adin ya cika. Kiyaye wa’adin na da muhimmanci wajen shigar da bayanai yadda ya dace da kuma tabbatar da gudanar da lamuran shirye-shiryen hajjin bisa tsari,” inji hukumar.

Akan haka ne daraktan ya shawarci maniyyata da sauran masu ruwa da tsaki da su kiyaye sanarwar da kuma bayar da haɗin kai ga wa’adin da hukumar ta sanya.

A cewarsa, hukumar na aiki tuƙuru wajen samar da ingantaccen hidima ga maniyyata da tabbatar da gudanar da harkokin hajjin cikin kyakkyawan tsari da kuma nasara.

By Babaji