Muna taimaka wa masu Umrah wajen samun ƙarin arziƙi — Baba Gambo

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban UBJ Group, Uzairu Baba Gambo ESK, ya bayyana cewa an kafa kamfanin ne domin taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin al’ummar Nijeriya, musamman masu gudanar da harkokin Makka da Umrah.

Uzairu Baba ya ce kamfanin na daga cikin masu gudanar da harkokin da suka samu amincewar hukumomin da abin ya shafa wajen taimaka wa maniyyata da masu Umrah wajen samun kayayyakin da suke buƙata a Makka, Madina da sauran wurare a ƙasar Saudiyya, da kuma a Nijeriya.

Ya ce mutanen da suka yi hulɗa da kamfanin na iya samun riba mai yawa tare da samun damar gudanar da harkokin biza cikin sauƙi.

Ya bayyana cewa dalilin da ya sa suka kasance a Kano shi ne domin wayar da kan jama’a game da ayyukan kamfanin, ta yadda za su samu damar cin gajiyar ayyukan UBJ a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Uzairu Baba ya ƙara da cewa sun samu shaidun gamsuwa daga mutane da dama waɗanda suka yi hulɗa da kamfanin, lamarin da ya ce ya ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen faɗaɗa ayyukansu.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron Hun Eɗpo da aka shirya a Kano, wanda ya samu halartar hukumomi, ƙungiyoyi da cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkokin aikin Hajji da Umrah.

An gudanar da taron ne ranar Asabar da ta gabata, inda mahalarta suka tattauna kan hanyoyin bunƙasa harkokin da suka shafi aikin Hajji da Umrah da kuma yadda za a inganta hidimar da ake yi wa maniyyata.

A ƙarshe, shugaban gudanarwa na UBJ Group ya bayyana cewa duk wanda ya yi hulɗa da kamfanin zai ga kyakkyawar mu’amala da ƙwarewa wajen gudanar da harkokinsu.

Ya yi kira ga al’umma da hukumomi da su ba da haɗin kai domin ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin al’umma da ci gaban Kano da Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply