Dangote na burin samun Dala biliyan 100 duk shekara nan da 2030

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa, kamfanin zai iya cimma burinsa na samun Dala biliyan 100 a matsayin kuɗaɗen shiga a duk shekara nan da shekarar 2030.

Dangote ya ce, cikakken nazari da ƙididdigar cikin gida da mahukuntan kamfanin suka gudanar ya ƙara musu tabbacin wannan buri na samun Dala biliyan 100 a shekara cikin shekaru huɗu masu zuwa abu ne da za a iya cimmawa. Ya bayyana hakan ne yayin da manyan jami’an Goldman Sachs, ɗaya daga cikin fitattun bankunan zuba jari da kamfanonin hidimomin kuɗi na duniya, suka kai ziyara matatar man fetur ta Dangote, da katafaren rukunin masana’antun sinadaran man fetur da takin zamani da ke Legas.

Tawagar Goldman Sachs, wadda Anthony Gutman, Mataimakin Shugaban Hukumar Gudanarwa kuma Shugaban Haɗin gwiwar Bankin Zuba Jari na Duniya na Goldman Sachs International ya jagoranta, ta zagaya Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals, Dangote Fertiliser Limited da sauran muhimman ababen more rayuwa da ke cikin rukunin masana’antun yayin ziyarar da ta kai Nijeriya.

Dangote ya ce hasashen kuɗaɗen shiga da kamfanin ya yi ya dogara ne kan ƙididdiga masu taka-tsantsan, lamarin da ya ƙara wa mahukuntan kamfanin kwarin gwiwar cewa za su iya tsara wani shirin bunƙasa kasuwanci mafi girma a dogon lokaci.

Ya kuma ce yadda ma’aikatan kamfanin suka nuna sha’awar saka hannun jari a sayar da hannayen jarin matatar Dangote ga masu zuba jari masu zaman kansu na baya-bayan nan, ya nuna irin ƙwarin gwiwar da suke da shi kan dabarun bunƙasa kamfanin da makomarsa.

Dangote ya bayyana matatar da sauran masana’antun da ke ƙarƙashin rukunin a matsayin misali na yadda zuba jari na dogon lokaci zai iya sauya tattalin arzikin Afirka, yana mai cewa burin bunƙasar rukunin ya zarce shirin da yake da shi na yanzu.

“Ko ta yaya za mu yi ƙoƙarin bayyana abin da muka gina, ba za ku iya fahimtar cikakken girmansa ba sai kun gan shi da idanunku. Amma wannan farkon tafiya ne kawai. Dole ne mu duba bayan 2030. Mataki na gaba na tafiyarmu zai ƙunshi sabbin zuba jari da kuma sayen wasu kamfanoni, yayin da muke ci gaba da faɗaɗa kasuwancinmu,” inji shi.

Bayan kammala rangaɗin da suka yi a katafaren matatar da ke da ƙarfin tace gangar ɗanyen mai 700,000 a kowace rana, jami’an Goldman Sachs sun yaba da irin abin da Dangote da ma’aikatansa suka cimma.

Sun ce, “Abin da Mista Dangote da ɗaukacin ƙungiyar suka cimma abin mamaki ne. Burin da suke da shi, girman aikin, ingancinsa da kuma tsarin aikin ma’aikatan abin burgewa ne ƙwarai.”

By ukarofi

Leave a Reply