Daga RABIU SANUSI a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, CON, ya bayyana cewa tsaron kowace ƙasa yana farawa ne daga kare rayuka, walwala da jin daɗin al’ummarta, yana mai jaddada cewa tsaro bai tsaya kawai kan kare iyakokin ƙasa ba.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake matsayin uban taron wata gagarumar ƙungiyar ƙa’idar Dokokin Jinƙai ta Duniya da Kwalejin Shari’a ta Jami’ar Northwest Kano suka shirya, inda ya gabatar da babban jawabi mai taken “Jagoranci, Zaman Lafiya da Rawar da Cibiyoyin Gargajiya ke Takawa wajen gina ƙasa.”
Mai Martaba ya bayyana cewa bai kamata a kallin rashin tsaro daga fuskar hare-haren makamai ko kare iyakokin ƙasa kawai ba, yana mai cewa mutanen da ba su da damar samun abubuwan buƙatun yau da kullum su ma suna fuskantar rashin tsaro.
Ya bayar da misalin mace da ba ta samun kulawar juna biyu, yaron da aka hana damar samun ilimi, da matashin da ba shi da aikin yi, a matsayin mutanen da ke fuskantar wani nau’i na rashin tsaro.
A cewarsa, yawancin ƙalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta a yau suna da alaƙa da sakaci wajen gina muhimman ginshiƙan da ake buƙata domin samar da al’umma mai cikakken tsaro. Don haka ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su mai da hankali kan alamomin farko na matsaloli tare da magance ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziƙi tun kafin su rikiɗe zuwa manyan barazanar tsaro.
Sarkin Sanusi ya kuma yi kira ga al’umma da su ɗauki tsattsauran mataki wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da masu fataucin ƙwayoyi, musamman ganin yadda matasa ke cikin haɗarin shiga aikata laifuka. Ya jaddada cewa gwamnati da hukumomin gargajiya dole ne su haɗa hannu wajen kare matasa da kuma samar da yanayin da zai ba su damar taka rawa mai kyau wajen ci gaban al’umma.
A nata jawabin, Mataimakiyar Shugabar Jami’ar Northwest, Kano, Farfesa Amina Salihi Bayero, ta yaba wa Sarkin bisa tawali’u da kuma jajircewarsa wajen neman ilimi, musamman yadda yake shirye ya zauna a cikin aji tare da sauran ɗalibai. Ta bayyana wannan mataki a matsayin babban abin ƙarfafa gwiwa ga ɗalibai da kuma saƙo mai kyau ga al’umma baki ɗaya, tana mai cewa neman ilimi ba shi da iyakar shekaru.
Babban bako mai jawabi kuma Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwa da Jama’a, Sunday Akin Dare, CON, ya gabatar da lacca mai taken “Zaman Lafiya, Jagoranci da ina ƙasa,” inda ya yi nazari kan alaƙar da ke tsakanin zaman lafiya, tsaro, shugabanci da ci gaban ƙasa.
Dare ya bayyana cewa Nijeriya da Afirka ba wuraren da suka rasa mafita ba ne, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da shugabanni da su koyi darussa daga tarihin da suka gabata, tare da yin aiki wajen gina cibiyoyi masu ɗorewa waɗanda aka kafa bisa adalci, daidaiton haƙƙoƙi, adalcin jinƙai, zaman lafiya da mutunta bil’adama.
A nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Shari’a, Mataimakin Farfesa Ahmad Jibrin Suleiman, ya gode wa manyan baki da mahalarta taron bisa amsa gayyatar da aka yi musu. Ya jaddada buƙatar koyar da matasa jagoranci ta hanyar misali da kyakkyawan ɗabi’a, maimakon dogaro da kalamai kawai, yana mai bayyana Sarkin Sanusi a matsayin abin koyi da kuma tushen ƙwarin gwiwa ga matasa.
ƙungiyar ƙa’idar Dokokin Jinƙai ta Duniya ta kuma karrama Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da lambar yabo saboda ƙwarewarsa wajen neman ilimi da kuma ɗabi’arsa; yayin da aka karrama Sunday Akin Dare saboda hidimarsa ta sadaukar da kai ga bil’adama da ƙasa.
Haka kuma an karrama Farfesa Amina Salihi Bayero saboda jagorancinta da sauye-sauyen da ta kawo a jami’ar, yayin da aka bai wa Kabiru, ɗaya daga cikin jami’an tsaron jami’ar, lambar yabo saboda ƙwazon da ya nuna wajen gudanar da aikinsa.
