Gwamnatin Enugu ta fara aikin samar da lantarki na sama da awanni 20 kullum

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Enugu ta fara wani garaumin aikin gina sabbin layukan rarraba wutar lantarki guda uku masu ƙarfin 33KV, da nufin inganta samar da hasken wutar lantarki mai ɗorewa, sauƙin samu da kuma inganci a wasu yankuna na jihar.

Aikin, wanda zai samo wuta daga Tashar Wutar Lantarki ta Ugwuaji, zai amfani al’ummomin ƙananan hukumomin Nkanu East, Nkanu ta Yamma, Aninri da Awgu.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, kafin ƙaddamar da aikin, an gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan harkar wutar lantarki a Cibiyar Taro ta ƙasa da ƙasa da ke Enugu ranar Asabar.

Da yake jawabi a wajen taron, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Jihar Enugu (ESEA), Christopher Ezeoha, ya ce aikin na da nufin magance matsalolin rashin isasshiyar wutar lantarki da al’ummomin yankin suka shafe shekaru suna fama da su.

Ezeoha ya ce ƙananan hukumomin Nkanu East da Nkanu West sun daɗe suna samun ƙarancin wutar lantarki saboda layin wutar guda ɗaya ne ke rarraba wuta zuwa wani yanki mai faɗi sosai.

Ya bayyana cewa layin Amechi 33KV yana samar da wuta ga ƙananan hukumomi takwas — biyar a Jihar Enugu da uku a Jihar Ebonyi — tare da tsawon fiye da kilomita 640.

A cewarsa, tsawon wannan layi na sa gano matsalar wuta da gyara ta cikin gaggawa ya zama abu mai wahala, lamarin da ke jawo dogon lokaci ba tare da wutar lantarki ba.

Ya ce wasu al’ummomi, ciki har da Nkerifi, Nara da Mburubu, sun kwashe fiye da shekaru 20 ba su da wutar lantarki. Ezeoha ya ce gwamnatin jihar ta umarci hukumar da ta dawo da wutar lantarki ga irin waɗannan al’ummomi, amma gyaran tsohon layin kaɗai ba zai magance matsalar ba.

Ya ce saboda haka gwamnati ta yanke shawarar raba dogon layin zuwa gajerun sassa ta hanyar gina sabbin layuka kusan uku, wanda kowannensu zai kasance da tsawon kusan kilomita 200 ko ƙasa da haka.

Haka kuma, za a girka tashoshin sauya ƙarfin wuta (injection substations) domin sauya wutar daga 33KV zuwa 11KV, abin da zai taimaka wajen ƙara inganci da ɗorewar wutar da al’ummomin ke samu.

Ezeoha ya ce burin gwamnatin jihar shi ne, bayan kammala aikin, al’ummomin da abin ya shafa su riƙa samun wutar lantarki na sama da sa’o’i 20 a kowace rana. Ya ce aikin ba zai tsaya kan waɗannan ƙananan hukumomi huɗu kawai ba, domin ana shirin faɗaɗa irin waɗannan matakai zuwa wasu sassan jihar, ciki har da Nsukka da Uzo-Uwani.

Ezeoha ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na shirya kayayyakin rarraba wutar lantarkinta domin samun damar karɓar wuta daga wata tashar samar da lantarki mai ƙarfin megawatt 630, wadda ake shirin ginawa a jihar. Ya ce babban burin gwamnati na dogon lokaci shi ne samar da wutar lantarki awa 24 a rana, kwana bakwai a mako.

By ukarofi

Leave a Reply