An kama budurwa a Kebbi kan zargin satar jariri da juna biyun bogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi, ta ce ta kama wata mata mai shekaru 19 a Ƙaramar Hukumar Zuru da ke jihar bisa zargin ta da sace wani sabon jariri da gabatar da shi ga mijinta a matsayin nata.

Al’amarin ya auku ne a ranar 23 ga Yuli, 2025, a lokacin da wadda ake zargin ta ziyarci wata mai suna Fatima Muhammad jim-kaɗan bayan ta haihu, inda ta taimaka mata da wasu ayyuka ciki har da ɗebo ruwa.

A cewar ‘yan sanda, wadda ake zargin ta yi amfani da damar hakan ne wajen tserewa da jaririn a madadin dawowa da ruwan da ta yi iƙirarin zuwa ɗebowa, lamarin da ya jafe ainihin mahaifiyar jaririn cikin tashin hankali.

Bincike ya nuna cewa, wadda ake zargin ta shiga halin matsi na rashin samun haihuwa, musamman ganin yadda sa’anni da abokan zamantakewarta suka samu.

‘Yan sanda sun ce, an zarge ta da yaudarar mijinta na tsawon kusan wata tara da sunan cewa tana ɗauke da juna biyu, kuma bayan haihuwar wancan jaririn, sai ta sace ta kai masa a matsayin ɗansa. Daga bisani, an kama ta a ranar 14 ga Agusta bayan ‘yan sanda sun gudanar da bincike kan al’amarin. Sannan, jami’an sun ƙwato jaririn sun damƙa shi ga mahaifiyarsa ta asali.

A cewar rundunar, jami’anta na tsare da matar, wadda da zarar an kammala bincike akanta, za a maka ta a kotu domin ta fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Akan haka ne Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Haɗejia ya yaba wa jami’an nasu bisa jajircewa da nuna ƙwarewa wajen ceto jaririn cikin aminci da kuma kama wadda ake zargi, yana mai tabbatar wa al’umma cewa za su cigaba da ƙoƙarin tabbatar da bayar da kariya ga yara da gurfanar da wanda aka samu da laifi a gaban shari’a, kamar yadda kakakinta SP Bashir Usman ya fitar a sanarwar mai ɗauke da 16 ga Agusta, 2026.

By Babaji

Leave a Reply