Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Maha da mutanen sa sun kashe mutum bakwai a ƙauyen Guru garin Sukuntuni na ƙaramar hukumar Kankia.
A hira da yayi a wata kafar sadarwa ta JBC Malam Abubakar Tijjani daga garin Sukuntuni ya bayyana cewa Kachalla da mutanen sa sun shiga gida gida su kai ta harbin mutanen ƙauyen tare da Kona Gidaje.
Yace wannan hari da Kachalla ya kai a ƙauyen ramakon gayyace domin a kwanakin baya sun shiga ƙauyen da niyar satar dabbobi amma mutanen ƙauyen su kai fito na fito da ‘yan bindigan har ta kai ma ɗan bindiga da ya ya rasa ransa.
Malam Abubakar ya ƙara da cewa bayan mutuwar ɗan bindigan, Kachalla ya me ayi zaman Sulhu da mutanen ƙauyen,amma bisa shawarar hukuma, mutanen ƙauyen suka ki amincewa da haka.
Ganin haka kamar yadda ɗan mai garin ya faɗa, Kachalla sai ya sake dawowar ɗaukar fansa da ta kaima har ya kashe mutane bakwai da ƙona gidaje.
Kafin haka ya faru a kwanakin baya a cewar sa ‘yan bindigan sun kashe Manoma uku a gonakin su.
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu jami’an tsaro ko hukumar da ta kawo masu ɗauki wanda hakan ya sanya yawancin mutanen ƙauyen da na garin Sukuntuni sun gujewa yankin.
Malam Abubakar ya bayyana takaicin sa kan yadda mazauna yankin su kai ƙorafi ga hukumomi gwamnati amma suka ƙi shiru.
