Mu na nazarin sakamakon zaɓen Osun – APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta ce tana nazari kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar na 2026 da aka kammala a kwanan nan, domin tantance matakin da za ta ɗauka na gaba.

Daraktan yaɗa labaranta, Kola Olabisi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a Osogbo.

A cewarta: “Babu yadda za a yi a ce an kammala zaɓe ba tare da aiwatar da dukkan damar da doka ta bayar ba na gyara ababen da suka saɓa wa tsari da aka gano yayin haka, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.”

Jam’iyyar ta ce za ta tattauna da lauyoyinta kan yiwuwar amfani da hanyoyin shari’a da doka ta tanada, ciki har da kai ƙara kotun zaɓe, Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli.

Ta kuma yi kirayi magoya bayanta da su kwantar da hankali, kuma su guji dukkan wani abin da ka iya haifar da rikici, tare da tabbatar da cewa za ta bi doka wajen neman haƙƙinta.

A safiyar ranar Lahadi ne Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Adeleke na jam’iyyar Accord Party a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’a 511,067, lamarin da ua ba shi damar doke abokin karawarsa na APC, Bola Oyebamiji da ya samu ƙuri’a 444,815. Najeem Salaam na ADC da ya zo na uku, ya samu ƙuri’a 17,180.

By Babaji

Leave a Reply