Ana zargin rufe otel ɗin Sandaji a Lafia na da alaƙa da siyasa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Rufin wucin gadi na otel ɗin Sandanji da ke Lafia wanda Alhaji Abubakar Shehu Usman na rukunin kamfanonin Sandanji Group of Companies ke mallaka ya haifar da ayar tambayoyi kan ko wannan matakin gwamnatin jihar lamari ne na tsaftar muhalli kawai ko kuma yana da alaƙa da siyasa.

A kwanan nan ne dai gwamnatin jihar ta Nasarawa ta ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta rufe otel ɗin bayan wani ambaliyar ruwa da ya auku a kewayen wurin da otel ɗin ya biyo bayan wani ziyarar duba da ido da kwamishiniyar ma’aikatar muhallin ta jihar Hon. Margret Elayo ta kai yankin jim kaɗan da aukuwar ambaliyar.

Da yake magana kan lamarin mai otel ɗin Alhaji Abubakar Shehu Usman yace har yanzu bai samu wata takarda a hukumance da ke bayanin dalilin rufe masa otel ba. Ya ce ko da yake kwamishiniyar ta duba wurin da ambaliyar ta shafa inda ta kuma umurci a rufe otel din na wucin gadi sai dai bai iya tantancewa ko rufewar ya shafi keta dokokin tsafta ne ko kuma saboda ambaliyar ruwan ne ba.

Dangane da haka ɗan kasuwar yace ambaliyar ruwan ba ta shafi ginin hotel ɗin ba, yana mai cewa ruwan bai ma shiga cikin otel ɗin ba kuma bai lalata wani kaya ba. Ya ƙara da cewa ruwan ambaliyar ya fito ne daga ɓangarorin daban-daban a yankin musamman daga yankin rukunin gidajen Abdullahi Adamu Estate da wani gangare sai ya taru a titunan da ke kusa da otel ɗin.

Usman yace tsarin ambaliyar ya kasance ba na al’ada ba yana mai lura da cewa ba a taba ganin irin wannan taruwar ruwa a yankin ba tsawon shekaru 25. Ya kuma nuna cewa wata ƙila an toshe hanya ko an gina bango da ya takura hanyar ruwa wanda hakan ya janyo karkatar da ruwan zuwa titunan dake maƙwabtaka. Duk da haka ya jaddada cewa lamarin ba ya da wata alaƙa da otel ɗin da kansa.

Ya kuma musanta zargin cewa otel ɗin Sandanji ya yi sakaci da dokokin tsaftar muhalli inda yace kamfanin na biyan kuɗin daukar sharar gida ta hanyar masu ɗaukar sharar da aka yi wa rijista kuma an tsaftace wurin sosai watan da ya gabata. Ya jaddada cewa otel ɗin ba ya zubar da sharar gida a cikin magudanan ruwa dake kewayen wurin.

Mai otel ɗin ya kuma yarda cewa wasu mazauna yankin kan zubar da sharar gida a yankin wanda haka nan ma jami’an tsafta ke amfani da shi wajen tattara shara. Yace hotel ɗin na bin ƙa’idojin tsaftar muhalli kuma kasuwancin ya yi rijista yadda ya kamata tare da sabunta takardu a hukumomin raya birane da kuma cibiyar NAGIS da sauran su.

Duk da cewa shi mai otel ɗin yana cikin jam’iyyar adawa ce a jihar ta Social Democratic Party (SDP) kuma yana da alaƙa da tsohon sufeton ‘yan sanda Alhaji Mohammed Adamu, Usman yace a yanzu ba ya tunani cewa rufin na da alaƙa da ramuwar gayya ta siyasa.

Ya bayyana kwamishiniya Margaret Elayo a matsayin ‘yar uwarsa yayin da gwamna Abdullahi Sule kuma abokinsa ne duk da bambancin siyasarsu inda yace ya na da yaƙinin gwamnatin jihar na da wani dalili mai ƙarfi da ta yi amfani da shi wajen ɗaukar wannan mataki.

By ukarofi