WAEC na fuskantar sabon ƙalubale kan sakamakon jarrabawar 2026 yayin zargin saɓa wa dokoki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Shirya Jarrabawar Yammacin Afirka (WAEC), ta fara fuskantar bincike kan sakamakon da ta fitar a kwanan nan na jarrabawar kammala sakandare ta WASSCE ta 2026 yayin da jagororin makarantu da masu kira ga neman ilimi suka yi zargin saɓa wa ƙa’idoji da matsalolin sadarwa sanadiyyar amfani da cibiyoyin kwamfuta (CBT).

Hakan na zuwa ne bayan da jagororin makarantu da dama suka yi ƙorafi da iƙirarin da masu kira ga neman ilimi suka gabatar cewa wasu zaƙaƙuran ɗalibai sun samu maki ƙasa da yadda ake tsammani, bisa la’akari da ƙoƙari da kuma abin da rahotannin karatunsu suka nuna.

A wata hira da Daraktan makarantar Impact House Model Schools da ke Mowe a Jihar Ogun, Sam Abdulazeez ya yi da manema labarai, ya ce sun gano cewa an samu gazawa a ƙoƙarin ɗalibai idan aka kwatanta sakamakon WASSCE na 2025 da na 2026 duk da cewa ya inganta walwalar malamai da kayan karatu da kuma lamuran shirye-shiryen jarrabawa.

Ya bayyana cewa, tun a 2017 ne makarantar take samar da ɗaliban WASSCE kuma suna fita da sakamako mai matuƙar kyau, musamman a darussan Lissafi da Turanci. Ya tunatar da cewa a 2024, baki ɗaya ɗalibai 45 da suka gabatar, sun samu A1 a Lissafi.

A cewarsa, al’amura sun sauya bayan gabatar da tsarin amfani da kwamfuta wajen rubuta jarrabawar a ‘yan shekarun baya, yana mai cewa baki ɗaya ɗalibansu a wannan shekarar sun samu maki 200 a jarrabawar UTME zuwa sama, wadda dama ta kwamfuta ake yin ta.

By Babaji

Leave a Reply