
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya yi gargaɗi ga hukumomin tsaro kan dogaro da aikin tura jami’an tsaro bayar da kariya wuraren zaɓuka yayin da ake gab da farawa, yana mai cewa samun hakan ya inganta na buƙatar a ɗauki tsawon watanni ana kimtsawa.
Janar Musa ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabin babban baƙo a taron Karramawa na jaridar Blueprint kan tsaro. Ya ce, wajibi ne a mu’amalanci al’amarin tsaron zaɓe wajen ɗaukar tsawon lokaci ana nazari a kai musamman don kimtsawar wuri da ƙoƙarin neman hanyoyin magance matsalolin da ka iya bijirowa ba wai a taƙaitu ba kaɗai a ranar zaɓe.
Ya bayyana cewa: “nasarar tsaron zaɓe ba ta samuwa ta tura jami’ai yayin da ake gab. Ana samu ne ta ɗaukar watanni ana shiri, ƙaddamar da atisayen leƙen asiri, haɗin-gwiwar hukumomi, ingantacciyar sadarwa da cigaba da nazari kan barazanar ababe masu tasowa da kuma uwa uba samun yardar al’ummar da aka ɗora wa alhakin yi wa hidima.”
Ya ƙara da cewa, sauyin yanayin ƙalubalen tsaro ya sa wajibi ne a riƙa shirya wa tsaron zaɓuka sama da kariyar rumfunan zaɓe, yana mai cewa barazanar tsaro ka iya samuwa ta yanar gizo, labaran bogi, matsin tattali da tauye ‘yancin ƙabila ko addini.
Kazalika, Janar Musa ya yi gargaɗin cewa baya ga mutum ya ɗauki makami ya je rumfar zaɓe, akan iya samun wani mai amfani da kafafen sadarwa ya yaɗa jita-jita da ka iya haifar da firgici acikin al’umma.
Har ila yau, Ministan ya bayar ginshiƙan cimma nasara wajen ƙarfafa tsaron zaɓuka guda shida da suka haɗa da amfani da dabarun leƙen asiri a matsayin abu na farko, amfani da kayayyakin fasaha a mafi yawan ayyukan da za a gudanar; haɗin-gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula.
Sauran sune: haɗin-gwiwa tsakanin sauran hukumomin tsaro; dabarun sadarwa na bai-ɗaya saboda ƙauce wa yaɗa labaran bogi; samar da yanayin harkar yaɗa labarai mai ƙarfi da kuma damawa da ‘yan ƙasa, yana mai cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya yaƙar ayyukan yaɗa labaran bogi ba.
