Sarkin Katsina ya sanar da naɗin sabbin Hakimai guda takwas

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Fadar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dakta) Abdulmumini Kabir Usman ta sanar da naɗin sabbin hakimai guda takwas a masarautar Katsina.

Sarki Usman, ya umarci sakataren majalisar masarautar Katsina Alhaji Isah Ali Kankia da ya bayyana naɗin sabbin hakiman, waɗanda za ayi bikin naɗin a ranar 29 ga Agusta, 2026.

Hakiman da za’a naɗa sun haɗa da Alhaji Sani Tukur Mu’azu Sarkin Rumah Katsina -( Hakimin Batsari
Da Alhaji Abba Lawal Sani Dutsi (Gabasawan Katsina)Hakimin Dutsi, Sai Alhaji Gambo Abdullahi Dabai (Dausayin Katsina) – Hakimin Dabai akwai kuma Alhaji Zakari Maina (Dan Yusufan Katsina)Hakimin Bindawa.

Da Alhaji Sanusi Kabir Usman (Karshin Katsina) – Hakimin Shinkafi da
Alhaji Abdurrahshid Nuhu Yashe (Bebejin Katsina) – Hakimin Kusada sai tsohon minista Sanata Hadi Abubakar Sirika (Marusan Katsina) – Hakimin Shargale.

Da kuma Alhaji Ibrahim Bello Kogo – Sarkin Kogon Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply