Sani Tadurga zai jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Jam’iyyar ADC a jihar ta tsayar da Honarabul Sani Tadurga a matsayin wanda zai jagoranci yaƙin neman zaɓen ta mai zuwa.
Wannan ya biyo bayan wani zama da masu ruwa da tsaki suka gudanar a garin Birnin Kebbi ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Alhaji Abubakar Chika Malami SAN ranar Talatar da ta gabata.
Da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja shugaban jam’iyyar ADC a jihar Kebbi Injiniya Sufiyanu ya bayyana cewa
Honarabul Sani Tadurga wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi ne kuma jigo a siyasar jihar kuma duk an amince da wannan matakin ba tare da wani jayayya ba.
A ƙarƙashin sa akwai mataimaka guda uku da suka suka fito daga kowace gundumar sanata a jihar suka haɗa da Arch. Bala Sani Kangiwa gundumar Kebbi ta Arewa, Hon. Shehu Aliyu Sambawa daga gundumar Kebbi ta tsakiya, Alh. Aliyu Jibrin Bagaruwa daga gundumar Kebbi ta Kudu sai kuma Aminu Bunza a matsayin Sakatare.
Ya ƙara da cewa an yi wannan tsarin ne kan cancanta da kuma sanin irin ƙwazon waɗannan mutanen bisa ga zummar za su gudanar da aikin da aka dora musu domin samun nasarar cin zaɓe in sha Allahu.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ADC ta shirya tsaf don shiga zaɓen game-gari mai zuwa don kawo sauyi da zai ceto al’ummar ƙasar nan.

By ukarofi

Leave a Reply