Yari ginshiƙi ne wajen samun nasarar Tinubu – Sani Shinkafi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Fitaccen jigon APC kuma jagoran siyasa, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce Sanata Abdulaziz Yari yana da darajar tsarin da ake buƙata don sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Shinkafi ya yi gargaɗin cewa nasara a Arewa maso Yamma ta dogara ne da ɗaukar mataki mai tsauri kan ‘yan ta’adda da kuma inganta samar da walwala ga ‘yan ƙasa.

Shinkafi ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da membobin ƙungiyar siyasarsa, “Wamban Shinkafi Democratic Front”, wanda aka gudanar a gidansa da ke Gusau, Jihar Zamfara.

Shinkafi ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta samu karɓuwa a yankin Arewa maso Yamma idan gwamnatocin tarayya da na jihohi suka fuskanci rashin tsaro kai tsaye.

“APC za ta iya samun nasara ne kawai a Arewa maso Yamma idan gwamnatocin tarayya da na jihohi suka yaƙi ‘yan ta’adda don samun zaman lafiya,” in ji Shinkafi.

Ya yi kira musamman ga Shugaba Tinubu da ya ba tsaro a Arewa maso Yamma fifiko sosai.

Ya lura cewa al’ummomi a Zamfara, Sokoto, Katsina da sauran jihohi na ci gaba da fama da hare-haren da ke kawo tarnaki ga shugabanci da ci gaban Kasa.

Shinkafi ya kuma buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya shiga tsakani ta hanyar inganta walwalar ‘yan ƙasa don rage wahalhalun zamantakewa da tattalin arziki da ke addabar jihar kafin zaɓen 2027.

A cewarsa, magance talauci da wahala yana da matukar muhimmanci idan jam’iyya mai mulki tana fatan samun nasara da kuma samun amincewar jama’a.

Dr. Shinkafi ya taya Sanata Abdulaziz Yari murna kan naɗinsa a matsayin darakta janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana hakan a matsayin abin da ya cancanta.

Ya shawarci Yari da ya gudanar da kamfen mai haɗaka tare da haɗa hannu da ƙarfe da dukkanin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen.

“Yari ya kamata ya saurari duk mambobi da magoya bayan APC a matsayin darakta janar na kamfen ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu don samun nasarar da ake buƙata,” in ji Shinkafi,

A cewarsa, haɗin kai a cikin jam’iyyar yana da mahimmanci don samun nasara.

Shinkafi ya bayyana kwarin gwiwar cewa tsarin siyasa da gogewar Yari a yankin yana ba APC fa’ida, amma sai idan an kiyaye haɗin kai da kuma samun amincewar jama’a musamman masu kaɗa ƙuri’a.

Dr. Shinkafi ya ƙara sanar da cewa ƙungiyar siyasarsa, (Wamban Shinkafi Democratic Front), tana goyon bayan kamfen ɗin sake zaɓen Shugaba Tinubu gaba ɗaya.

“Ƙungiyarmu za ta goyi bayan kamfen ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu don samun nasarar sa a 2027,” ya bayyana,

Ya yi kira ga ‘yan majalisar ƙungiyar sa ta Wamban Shinkafi Democratic front da su fara gangamin wayar da kan jama’a a faɗin Zamfara da Arewa maso Yamma don cimma burin nasarar APC.

By ukarofi

Leave a Reply