Shugaban NFF, Ibrahim Gusau da manyan jami’an hukumar sun yi murabus yayin binciken biliyan N17

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) tare da wasu manyan jami’an hukumar sun ajiye muƙamansu bayan ƙorafe-ƙorafen al’umma da kuma binciken wasu biliyoyin kuɗaɗe da aka ware don harkar ƙwallon ƙafa.

Jagorancin hukumar ya rushe ne bayan watanni yana fuskantar matsi kan rashin samar da kyawawan sakamako da nazarin kuɗaɗe.

Al’amarin ya caɓe ne a lokacin da ‘yan wasan Super Falcons suka gaza samun cancantar shiga gasar Kofin Duniya na Mata na 2027 da za a yi a Brazil, karo na farko da tawagar ta rasa damar tun bayan fara gasar a 1991 bayan da ta sha kaye a hannun Kamaru da Afirka ta Kudu. An shiga matuƙar ƙunci ne a lokacin da ita ma Super Eagles ta maza ta gagara samun gurbi a gasar Kofin Duniya sau biyu a jere.

A cewar jaridar Vanguard, takwas daga cikin tawagar manyan jami’an hukumar sha uku sun yi murabus, lamarin da ya jefa NFF cikin mawuyacin hali.

Hukumomin tsaro ciki har da DSS suna bincike kan yadda aka sarrafa kuɗin tallafi har Naira biliyan 17 da aka amince da ware su tun a shekarar 2024 domin biyan albashin ‘yan wasa da wasu kuɗaɗen ƙari. Jami’ai sun bayyana binciken a matsayin neman ba’asin yadda aka gudanar da kuɗaɗe da aka saba.

Duba da yadda jagoranci ya rushe, goben hukumar na halin rashin tabbas musamman ganin yadda ita ke da alhakin dukkan wani abin da ya shafi harkar ƙwallon ƙafa a Nijeriya.

Haka kuma, ana ganin wannan tsaiko ka iya shafa ko haifar da jinkiri ga zaɓen majalisar zartarwar NFF da aka shirya gudanarwa a ranar 27 ga Satumba, 2026 a Birnin Lafiyan Jihar Nasarawa.

By Babaji

Leave a Reply