An buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi su ja mataimakansu a jiki

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Kwamishinan ƙananan hukumomi da cigaban al’umma na Jihar Gombe, Barista Sani A.A. Haruna, ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi 11 da na yankunan cigaban ƙananan hukumomi (LCDA) da su riƙa bai wa mataimakansu muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin mulki.

Haruna ya yi wannan kiran ne a wajen taron ƙara wa juna sani da ma’aikatar ƙananan hukumomi da cigaban al’umma ta shirya domin shugabannin ƙananan hukumomi da LCDA na jihar.

Kwamishinan ya ce bai kamata shugabannin su mayar da mataimakansu saniyar ware ba, yana mai cewa sanya su cikin ayyukan gwamnati zai taimaka wajen inganta shugabanci da samar da cigaba a matakin ƙananan hukumomi.

Ya ce bai wa mataimakan shugabanni nauyin da ya dace zai rage zaman banza, ƙarfafa haɗin kai da kuma sauƙaƙa tafiyar da harkokin mulki.

Haruna ya kuma buƙaci shugabannin da su rungumi tuntuɓa da tattaunawa da mataimakansu, musamman wajen tsara da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da samar da hidimomin da al’umma ke buƙata.

Da yake nasa jawabin, shugaban ma’aikatan gwamnan Jihar Gombe, Abubakar Inuwa Kari, ya ce tafiyar da alaƙa tsakanin shugabanni da mataimakansu na daga cikin manyan ƙalubalen shugabanci da ke buƙatar haƙuri da dabara.

Kari ya shawarci shugabannin da su kasance masu fahimta da hakuri, tare da kauce wa ware mataimakansu daga ayyukan gwamnati, domin hakan na iya haifar da rashin jituwa da kawo cikas ga gudanar da mulki.

Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Gombe kuma shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON), Prof. Abdullahi Bappah Garkuwa, ya yaba wa gwamnatin jihar kan shirya taron, yana mai cewa yana taimakawa wajen ƙara fahimtar juna da inganta shugabanci.

Garkuwa ya kuma buƙaci gwamnati ta shirya irin wannan taro ga mataimakan shugabannin ƙananan hukumomi, domin su ma su ƙara fahimtar nauyin da ke kansu.

Ya tabbatar da cewa shugabannin ƙananan hukumomin jihar za su ci gaba da aiki tuƙuru wajen sauke nauyin da aka ɗora musu da yi wa al’umma hidima.

By ukarofi

Leave a Reply