Garkuwar Borgu: Har yanzu ba mu samu tattaunawa da ‘yan bindiga ba – Gwamnatin Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Neja ba ta samu wani kira daga ‘yan ta’addan da suka sace masallata ba a wani masallaci da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a ranar Juma’a, inji Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Neja, Obed Nuhu.

Nuhu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce harin ya faru ne a wurare guda uku da ke yankin, wanda ake zargin ƙungiyoyin Lakurawa da Boko Haram da alhakin ƙaddamarwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, kwamishinan ya ce har yanzu gwamnatin ba ta samu damar tattaunawa ba da masu garkuwar tun bayan faruwar al’amarin.

Haka kuma, kwamishinan ya ce gwamnatin ba za ta iya tabbatar da adadin waɗanda aka yi awon-gaba da su ba, inda har yanzu jami’ai suna ƙoƙarin gano ainihin yawansu. Sannan gwamnatin ba za ta dogara da zargi ba har sai ta tabbatar da bayanan da take ƙoƙarin tattarawa.

Bayan harin ne Gwamna Umaru Bago ya bayyana damuwarsa akan haka da kuma umartar hukumomin tsaro da su yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki don ganin an ceto mutanen cikin aminci tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da al’amarin ya afka wa.

Tuni dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su gaggauta fara atisayen bincike domin ceto mutanen da aka sace, kamar yadda kakakinsa Bayo Onanuga ya bayyana a wata takarda, ranar Talata.

By Babaji

Leave a Reply