Ndume ya buƙaci Tinubu ya kori ‘marasa ƙwarewa’ daga gwamnatinsa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire jami’an da ba su da kwarewa daga cikin gwamnatinsa, yana mai cewa kasancewarsu na jawo wa gwamnatin abin kunya.

Ndume, wanda tsohon shugaban marasa rinjaye ne a Majalisar Dattawa kuma jigo a jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ.

Ya ce abin da ya kira “kakistrocrats”, wato mutanen da ba su da kwarewa ko cancantar gudanar da mulki, na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da rikice-rikice da badakalar da ke addabar gwamnatin.

Sanatan ya yi nuni da badaƙalar wata hukumar gwamnati da ake zargin ƙarya ce, wadda ta yi aiki har ma da samun ofishi a harabar ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Ya yaba wa Tinubu kan matakin da ya ɗauka na dakatar da wasu manyan jami’an gwamnati da kuma ba da umarnin kama wanda ake zargin yana gudanar da hukumar.

Sai dai Ndume ya ce har yanzu shugaban bai ɗauki matakin da ya dace wajen magance matsalar rashin ƙwarewar wasu jami’an gwamnatinsa ba.

Ya ce da akwai mutane masu cikakken ƙwarewa a muƙaman gwamnati, da ba a samu irin waɗannan badaƙaloli da abubuwan kunya ba.

By ukarofi

Leave a Reply