’Yan sandan Abuja sun ƙaryata rahoton sayar da ƙodar matasa a Nyanya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ƙaryata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa matasan da ke zaune a yankin Nyanya sun sayar da ƙodarsu domin samun kuɗi, yayin da wani wakili a Mararaba ke sayen sassan jikin mutane.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta bayyana a Abuja ranar Laraba cewa rundunar ba ta samu ko tabbatar da wani rahoto makamancin haka ba.

Ta ce babu wata sanarwa ko saƙo da ya fito daga rundunar da ke tabbatar da zargin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da rahoton tare da kauce wa yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba.

Ta ce yaɗa irin waɗannan bayanai na iya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna FCT.

Sai dai rundunar ta buƙaci duk wanda ke da wani bayani game da zargin fataucin sassan jikin mutane ko wata matsalar tsaro a FCT da ya kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Rundunar ta kuma bayar da lambobin waya 07038979348 da 08028940883 domin kai rahoton duk wani lamari da ya shafi tsaro.

By ukarofi