Emmanuel Ikpeme ya zama babban sakataren NFF na riƙo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta kira taron gaggawa a Abuja bayan murabus ɗin Shugabanta Ibrahim Gusau da ‘yan kwamitin zartarwarsa a ranar Alhamis bayan matsi daga Hukumar kula da Harkokin Wasanni ta Ƙasa (NSC).

Majiyoyi sun ce akwai yiwuwar a soke gudanar da zaɓen NFF da aka shirya a 27 ga Satumba, 2026 a Lafia, Jihar Nasarawa, da samar da wani kwamiti da zai jagoranci gudanar da harkokin hukumar har zuwa lokacin da za a yi sabon zaɓe.

Bayan murabus ɗin Babban Sakataren, Dakta Mohammed Sanusi a ranar Alhamis, mataimakinsa, Dakta Emmanuel Ikpeme ne ya maye gurbinsa na wucin-gadi har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.

An ruwaito cewa, a ranar Alhamis ne Dakta Sanusi ya miƙa wa Ikpeme ragamar ofishin a hukumance a Abuja. An naɗa Ikpeme ne a matsayin ɓangare na matakan gudanar da harkokin NFF na yau da kullum zuwa lokacin da za a samu sabon shugabanci a ƙarƙashin hukumar.

By Babaji

Leave a Reply