
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci da a gudanar da gagarumin gyara a fannin harkokin ƙwallon ƙafan Nijeriya domin shawo kan matsalolin rashin nasara da tawagogin ‘yan wasa suka fuskanta a gasan matakan nahiya da na duniya.
Ya ce, wajibi ne gyaran ya ƙunshi ƙarfafa harkar shugabanci, gudanarwa, wakilcin masu ruwa da tsaki, ci-gaban damarmaki, wasannin gida da tabbatar da gaskiya da adalci a harkar ƙwallon Nijeriya.
Shugaban ya bayyana cewa, yayin da wasu wasanni suke samun nasarori tun bayan sake kafa Hukumar kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC), harkar ƙwallon na cigaba da fuskantar ƙalubale saboda gazawar tsare-tsare a fannin a matsayinsa na mafi shahara a wasannin Nijeriya.
Akan haka ne Tinubu ya umarci Shugaban NSC da ya yi aiki tare da ofishin NFF na ƙasa da wasu masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafa domin tabbatar da bunƙasa harkar gudanarwa da samar da ingantaccen tsarin gyare-gyare ta yadda za a maido da ƙwarin-gwiwa da martabarta a idon duniya.
Daga cikin hanyoyin gyaran akwai aiki da hukumomin FIFA da CAF yayin bayar da kariya ga wajiban Nijeriya a tsarin gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa-da-ƙasa.
Kazalika, Shugaban ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin da ‘yan Nijeriya da su bayar da gudunmawarsu ga sauyin da kuma yin aiki tare don ganin an samar da tsari mai cike da gaskiya da adalci da ƙoƙarin cimma nasarori.
