‘Yan sanda sun kama mutum biyu da zargin taimakon ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda da haɗin gwiwan ‘yan banga sun kama mutane biyu da ake zargi da taimakawa yan bindiga a ƙaramar hukumar Jibiya.

A wata sanarwa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa sanda suka tare wata Mota ƙirar Volkswagen Golf numba TFA 29 AA.

A bincike da suka gudanar sun gano direban motar mai suna Babangida Mohammed Yana ɗauke da wani mai suna Rabi’u Isah da wasu kaya da ake zargi za su kaiwa ‘yan bindiga a nan Jibiya.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa kayan sun haɗa da dozin shida na Black balbet, dozin biyu na Green belt, keken ɗinki, dozin na Zippers,kayan sawa da sauran su da ake zargin ana amfani da su a matsayin wajan ajiyar harsasai da wasu kayan yaƙi da yan bindiga ke amfani da su.

Yace waɗannan mutane biyu da ake kama sun tabbatar da cewa sun fito daga garin Kwatarkwashi a Jihar Zamfara.

Kwamishinan ‘yan sanda a Katsina CP Ali Umar Fage ya yaba wa jami’an sa kan ƙwarewa da suka nuna da ta kai su kama wanna mota.

CP Ali Fage ya Jaddada burin jami’an tsaro na tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma tare da tabbatar da tsaro a Jihar.

By ukarofi

Leave a Reply