Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da yin nuƙu-nuƙu kan batun cire tallafin man fetur.
Atiku ya ce gwamnati ba za ta ce ta kawo ƙarshen tallafin man fetur ba, alhali tana bai wa masu zuba jari a harkar man fetur rangwamen haraji, tallafin kuɗi da sauran gata na musamman.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, Atiku ya bayyana bikin da gwamnatin Tinubu ke yi kan cire tallafin a matsayin “ɗaya daga cikin manyan yaudarar tattalin arziki” da ake yi wa ’yan Nijeriya.
Ya ce yayin da talakawa ke fuskantar hauhawar farashin man fetur, sufuri da kayan abinci, gwamnati na ci gaba da rage wa manyan masu zuba jari a masana’antar man fetur haɗarin kasuwanci ta hanyar ba su rangwamen haraji da sauran tallafi.
Atiku ya kuma yi nuni da bayanan asusun NNPC, inda ya ce an kashe kusan Naira tiriliyan 4.84 a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 7.13 a shekarar 2024 kan abubuwan da aka bayyana da “energy security” da sauran gibin farashin man fetur.
Ya tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke cewa tallafin man fetur ya ƙare, alhali har yanzu ana amfani da kuɗin gwamnati wajen ɗaukar wasu daga cikin gibin farashin.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce shirinsa na Atiku Economic Recoɓery Plan ba ya nufin dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur da ya kira mara gaskiya da cike da almundahana ba.
A cewarsa, abin da yake son yi shi ne samar da tallafi mai iyaka, bayyananne kuma za a dinga binciken yadda ake kashe kuɗinsa, tare da ƙara tace danyen mai a cikin gida, inganta gasa da kuma samar da ingantaccen tsarin sufuri.
Atiku ya ce bai yi adawa da bai wa masu zuba jari gata ba, amma ya kamata a yi amfani da irin wannan tsarin wajen rage wa talakawa radadin tsadar rayuwa.
Ya bukaci gwamnati ta bayyana waɗanda ke cin gajiyar rangwamen haraji da sauran gata da ake bai wa masu zuba jari a masana’antar man fetur, da kuma adadin kuɗin da gwamnati ke rasa sakamakon hakan.
Ya ce ma’aunin nasarar gyaran tattalin arziki bai kamata ya zama yawan wahalar da ’yan kasa ke sha ba, sai dai ko rayuwarsu ta inganta, kasuwanci ya bunƙasa, an samar da ayyukan yi, kuma iyalai na iya biyan bukatun yau da kullum.
Atiku ya kuma jaddada cewa zai ci gaba da neman aiwatar da tsarin tallafin da aka yi niyya ga ’yan Nijeriya masu fama da tsadar rayuwa, duk da adawar gwamnatin Tinubu.
