Sarkin Katsina ya naɗa sabbin hakimai bakwai

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina ya naɗa sabbin hakimai bakwai ciki har da tsohon Ministan Sufuri Sanata Hadi Sirika a masarautar Katsina.

Naɗin wanda ya gudana a fadar Sarkin Katsina ya zo ne a wani mataki na ƙarfafa tsarin gudanar da harkokin masarauta da kuma inganta shugabanci a yankunan da hakiman ke jagoranta.

Hakiman da aka naɗa sun hada da Alhaji Sani Tukur Mu’azu Sarkin Rumah Katsina, Hakimin Batsari da Alhaji Abba Lawal Sani Dutsi Gabasawan Katsina, Hakimin Dutsi.

Saura sun haɗa da Alhaji Gambo Abdullahi Dabai Dausayin Katsina, Hakimin Dabai da
Alhaji Zakari Maina, Dan Yusufan Katsina Hakimin Bindawa.

Akwai Alhaji Sanusi Kabir Usman, Karshin Katsina – Hakimin Shinkafi sai Alhaji Abdurrahshid Nuhu Yashe Bebejin Katsina Hakimin Kusada da Kuma Alhaji Ibrahim Bello Kogo – Sarkin Kogon Katsina.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Farouk Lawal Jobe ya halarci bikin naɗin.

By ukarofi

Leave a Reply