
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jaddawalin sunayen ‘yan takarar gwamnan Jihar Nasarawa, inda aka ga babu sunan tsohon Sufeto-Janar na Rundunar ‘Yan sanda, Mohammad Abubakar Adamu a ciki.
INEC ta wallafa sunayen ‘yan takarar ne tare da jam’iyyun siyasar da ta tantance domin shiga zaɓen gwamna a jihar Borno.
A cewar jaddawalin, ‘yan takarar sune Ahmed Aliyu Wadada na All Progressives Congress (APC); Musa Adamu Angbazo na Social Democratic Party (SDP); Dahiru Musa Doma, Action People’s Party (APP); Jonathan Gaza Gbefwi, Labour Party (LP); Manjo Janar Nuhu Angbazoq (mai ritaya) na African Democratic Congress (ADC); Emmanuel David Ombugadu na Peoples Democratic Party (PDP); da Ibrahim Kasimu Aboh na All Progressives Grand Alliance (APGA).
Sauran sun haɗa da Christopher Mamman, Action Democratic Party (ADP); Abdullahi Omame Abisabo, Peoples Redemption Party (PRP); Abubakar Abdu Giza, Zenith Labour Party (ZLP); Mohammed Awwal Suleiman na Allied People’s Movement (APM); Abdullah Bukhari na Action Alliance (AA); Kigbu John Tanko, Young Progressives Party (YPP); Dogo Danladi Shammah, Nigeria Democratic Congress Party (NDC); da kuma Shuaibu Umaru Kubi of Accord.
Amma, Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban ‘yan sandan, Abdullahi Yammani ya yi watsi da cire mai gidan nasa, inda ya tabbatar da cewa Mohammad Adamu ya yi rajista da jam’iyyar SDP kuma za a kara da shi a zaɓen.
Yammani ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Lafia, wanda ya ce Adamu ya riga ya kammala rajista da SDP ta intanet bayan ficewa daga APC, inda ya faɗi a zaɓen fidda gwani.
