Iran ta yi martani a sansanin sojin Amurka na Jordan bayan harin ƙasar a tsibirin Larak

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iran ta ce ta ƙaddamar hare-haren makamai masu linzami a sansanonin sojojin Amurka guda biyu da ke ƙasar Jordan bayan da Amurkan ta kai farmaki akan Larak Island da ke kudancin Iran a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da hukumomin yaɗa labaran Iran suka fitar a ranar Lahadi, Dakarun Juyin juya halin Musulunci (IRGC), sun ce tagwayen farmakin da suka kira da “Punishment of the Aggressor”, sun sauka akan sansanonin King Hussein da Al Azraq a Jordan.

Musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu a rikicin nasu ya cigaba da aukuwa ne tun a ƙarshen Yuli bayan shirin yarjejeniyar tsagaita wuta da bai yi nasara ba.

IRGC ta ce harin nata ya lalata cibiyar kula da gyaran makamai da kuma wuraren da ake tura dakaru, wanda hakan ya yi gagarumin dameji ga ƙarfin sojin.

A wani ɓangare kuwa, Jordan ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami guda takwas jim-kaɗan bayan IRGC ta sanar da harin nata, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.

By Babaji

Leave a Reply