
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa hoɓɓasar dakarun tsaro wajen ceto ‘yan hidimar ƙasa ta hukumar NYSC guda 15 da wasu mutane shida da aka yi awon-gaba da su a Jihar Kogi.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro (DHQ) Manjo-Janar Michael Onoja ya fitar a ranar Litinin, ya ce mutane 21 da suka haɗa da maza takwas da mata 13 ne aka ceto a Dajin Egume-Ochaja.
Ya bayyana cewa, sojojin za su cigaba da ƙoƙari wajen ganin sun ceto mazauna yankin Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja da aka sace a kwanakin baya.
Da yake tsokaci kan wannan nasara a shafinsa na kafar X, Shugaba Tinubu ya ce ‘yan hidimar ƙasar, waɗanda aka ceto suna halin karɓar magani kafin daga bisani a damƙa su ga iyalansu.
Ya kuma jinina wa atisayen tawagar bincike da ceto na sojojin tare da yaba wa iyalai da makusantan waɗanda aka mutanen bisa fahimtarsu yayin mawuyacin halin da masoyan nasu suka shiga.
A ƙarshe, ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen magance matsalolin rashin tsaro a sassan Nijeriya yayin da hukumomin tsaro suke cigaba da ɗaura ɗamarar yaƙi da ayyukan ta’addanci a Nijeriya.
