Kwamitin zaman lafiya na ƙasa ya ziyarci ‘yan sandan Kano don ƙarfafa shirye-shiryen zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026 Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta karɓi baƙuncin tawagar Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa (NPC) ta hannun Sakatariyar The Kukah Centre, a babban ofishinta da ke Bompai a jihar.

An gudanar da ziyarar ne da nufin ƙarfafa harkokin zaman lafiya yayin zaɓukan 2027 ta hanyar haɗin-gwiwar masu ruwa da tsaki.

Mista Espom Ajanya, Ƙaramin Manajan Shirye-shirye na The Kukah Centre ne ya jagoranci tawagar. Da yake jawabi yayin ziyarar, Mista Ajanya ya bayyana cewa, wannan ziyarar ɓangare ne na shirye-shiryen kwamitin domin zaɓen 2027 ta yadda za su buƙaci haɗin-gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki da za su taimaka wa gudanar da zaɓukan cikin lumana da ƙaurace wa dukkan wani rikici da ka iya tasowa.

A cewarsa: “Mun zo nan ne domin tattauna halin zaɓe da tsaro a Jihar Kano, warware matsaloli masu tasowa, da faɗaɗa damarmakin da za su ƙarfafa wa zaman lafiya da tallafa wa gudanar zaɓen 2027 cikin aminci.” Tawagar ta kuma yaba wa rundunar ‘yan sandan Kano bisa ƙwarewarta, dabarun ɗaukar matakan kariya da ƙoƙarin samar da hanyoyin ɗorewar zaman lafiya da tsaro a jihar.

A nasa jawabin, Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi maraba da kwamitin, sannan ya bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci da aka yi a lokacin da ya dace, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya a lokaci da kuma bayan zaɓuka.

Ya kuma tabbatar wa tawagar cewa rundunar a shirye take ta yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da hukumomin tsaro, INEC da wasunsu domin tabbatar da lumana da zaman lafiya ga zaɓukan 2027, inda tuni rundunar ta fara horar da jami’ai kan lamuran tsaron zaɓe, kamar yadda kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana a wata takarda.

By Babaji

Leave a Reply