Wani Kirista ya gina masallacin Juma’a a Filato

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani Kirista mazaunin Jihar Filato, Peter Ibrahim Gyendyeng, ya gina wa al’ummar Musulmi Masallacin Juma’a a yankin Gana Ropp da ke ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a jihar.

Ginin masallacin ya faranta wa al’ummar Musulmin yankin rai, inda suka bayyana matakin a matsayin wata alama ta haɗin kai da kuma nuna cewa su ma suna da muhimmiyar rawa a cikin al’umma.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar Kiristoci da Musulmi a wasu sassan Jihar Filato ke fuskantar ƙalubale sakamakon rikice-rikicen da suka faru a yankin, musamman a ƙaramar Hukumar Barkin Ladi.

Da yake magana a wajen ƙaddamar da masallacin, Gyendyeng, wanda ya taɓa wakiltar mazaɓar Barkin Ladi/Bassa a Majalisar Wakilai ta Tarayya, ya ce ya gina masallacin ne domin ya zama wata alama ta zaman lafiya da haɗin kai tsakanin Kiristoci da Musulmi a yankin.

Ya ce bai wa mutane kuɗi na iya zama taimako na ɗan lokaci, amma gina musu wajen ibada wani aiki ne da zai ci gaba da amfani na dogon lokaci.

“Idan ka bai wa mutane kuɗi, za su kashe. Amma idan ka gina musu wajen ibada, za su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya da ci gaban ƙasa,” inji shi.

Babban Limamin masallacin, Sheikh Ladan Gana Ropp, ya gode wa Gyendyeng bisa wannan aiki, yana mai cewa ginin masallacin ya sa Musulman yankin sun ji cewa su ma ana ganin ƙimarsu kuma suna da matsayi a cikin al’umma.

“Mun yi farin ciki sosai lokacin da ya gina masallacin. Ba mu taɓa samun irin wannan aiki a yankin ba. Ya sa mun ji cewa mu ma muna da matsayi a cikin al’umma, kuma ba za mu taɓa mantawa da wannan abin alheri ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa Kiristoci da Musulmi sun haɗu a lokacin ƙaddamar da masallacin domin yi wa Gyendyeng, Jihar Filato da ƙasar baki ɗaya addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

Babban Limamin ya yi kira ga Kiristoci da Musulmi a Jihar Filato da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da haƙuri domin ƙarfafa fahimtar juna da kuma samar da zaman tare cikin lumana.

Fastoci, limamai da sauran mambobin al’ummar Kirista na daga cikin waɗanda suka halarci bikin ƙaddamar da Masallacin Juma’ar.

By ukarofi

Leave a Reply