Ya zama dole a mutunta haƙƙin El-Rufai —Majalisar ƙoli ta Shari’a

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar ƙoli ta Shari’a ta Nijeriya (SCSN) ta sake nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, tana mai cewa dole ne a mutunta haƙƙinsa tare da tabbatar da an bi ƙa’ida a shari’ar da ake yi masa.

A wata sanarwa da Sakataren-Janar na majalisar, Nafiu Baba-Ahmad, ya fitar, SCSN ta ce El-Rufai, kamar kowane ɗan Nijeriya, ana ɗaukar sa marar laifi, har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

Tsohon gwamnan na fuskantar shari’a kan zarge-zargen da suka haɗa da cin amanar ofis, zamba, bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba, halatta kuɗaɗen haram da kuma amfani da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake gwamnan Kaduna.

Haka kuma, Hukumar DSS na tuhumar sa kan tatsar wayar Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu.

Sai dai SCSN ta ce ba ta goyon bayan aikata laifi ko ta wane hali, amma ta jaddada cewa neman adalci shi ma dole ne ya kasance cikin adalci.

Majalisar ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da bin tsarin doka a kowane mataki, tare da guje wa duk wani mataki da zai iya sa a zargi hukumomi da musguna wa El-Rufai saboda siyasa.

Ta ce amincewar jama’a da hukumomin gwamnati na dogara ne da yadda ake aiwatar da doka cikin adalci, gaskiya da rashin nuna bambanci

By ukarofi

Leave a Reply