
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata gobarar tsakar dare ta yi sanadiyyar lalata shaguna, rumbuna da gidaje guda shida a kasuwar Ƙofar Wambai da ke Jihar Kano, lamarin da ya jefa ƙananan ‘yan kasuwa da mazauna cikin asara.
Al’amarin ya faru ne a daren Asabar a yankin Babban Layi, sashen ‘Yan Robobi na sananniyar kasuwar, inda aka samu jami’an kashe gobara sun yi ƙoƙarin daƙile cigaba da yaɗuwar gobarar zuwa wasu sassan kasuwar.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi, sashen agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:43 na dare daga wani Sufuritandan hukumar mai suna Usman Idris Fagge akan iftila’in. Akan haka ne jami’an hukumar daga Rijiyar Zaki, Sabon Gari, Gidan Gwamnati da Bompai suka gaggauta zuwa wajen sannan suka shawo kan al’amarin.
Ya bayyana cewa, a lokacin da suka isa wajen sun samu wani ginin bene mai hawa biyu da ke da faɗin ƙafa 120 zuwa 125 na ci da wuta. A sanadiyyar haka shaguna biyu da ke ƙasa suka ƙone, biyu a hawa na ɗaya, rumbuna shida da wasu huɗu na wucin-gadi a hawan ƙarshe dukkaninsu sun lalace.
Gidajen da iftila’in ya shafa kuma sun haɗa da na Alhaji Sani, Sani Muhammad, Alhaji Kwa Kwa, Alhaji Shafi’u da kuma na Alhaji Sulaiman.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas ya roƙi ƙananan ‘yan kasuwa da mazauna da su cigaba da kasancewa masu sanya ido da ɗaukar matakan kariya domin kauce sake samun irin haka a nan gaba, yana mai shawartar su da su riƙa ajiye tukunyar kashe wuta a kusa da su.
A wannan shekara, Jihar Kano ta fuskanci iftila’in gobara har sau biyar, inda a Singa kaɗai aka sami aukuwarta har sau biyu.
