Yadda kungiyar Triple R ta gudanar da taron Maulidi a Kano

Spread the love

Daga KHALID IMAM

A ranar Talata, 2 ga Satumba, 2026, ƙungiyar Triple R Kannywood Renewed Hope, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ta shirya gagarumin taron Maulidin Annabi (SAW) a harabar filin bajekoli na Aminu Ɗantata da ke Kano.

Alhaji Aminu Alfandaj, Shugaban Kwamitin Shirya Taron (LOC), ne ya jagoranci taron. An fara taron da karatun Alƙur’ani Mai Girma, sannan PRO na Triple R Kannywood Renewed Hope, Tijjani Asase, ya gabatar da jawabin maraba.

Taron ya ƙunshi nasihohi da tunasarwa masu ilmantarwa da jan hankali game da darajojin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama daga bakunan manyan malamai. An gabatar da waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAW), waɗanda suka mayar da hankali kan kyawawan halayensa, ɗabi’unsa da kuma rayuwarsa abar koyi.

Shugaban Ƙungiyar Triple R Kannywood Renewed Hope, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara yana daga cikin zaƙaƙuran mawaƙa masu yabon Ma’aiki SAW da suka gabatar da waƙoƙin yabo masu ƙayatarwa, waɗanda suka nuna irin girman ƙauna da girmamawa da yabo da ake yi aka yi wa Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW). Wasu daga cikin fitattun mawaƙan addinin Musulunci sun gabatar da waƙoƙi da salo mai ban sha’awa, inda suka bayyana ƙaunarsu da girmamawarsu ga Manzon Allah (SAW).

Da misalin ƙarfe 11:58 na safe, Malam Nafi’u Adam Sha’iri ya buɗe fagen waƙoƙin yabo, inda ya fara wani zama mai matuƙar taɓa zuciya da ƙara wa mahalarta kuzarin ruhaniya. Daga bisani Sayyada Faiza Amatullah, Sayyadi Sojan Ma’aiki, Sayyadi Malam Kabiru Kiya Ambato, Malam Mustapha Zakariya da Malam Ahmad Gwangwazo, da sauran fitattun mawaƙa, suka biyo baya.

Fitattun sha’iran waƙoƙin yabon Annabi (SAW), ƙarƙashin jagorancin Sheikh Hafiz Abdalla da Malam Bashir Ɗandago, su ma sun ƙara armashi da muryoyinsu da baitocin waƙoƙi masu ratsa zuciya. Sha’iran sun bayyana kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW) da ɗabi’unsa, falalolinsa marasa misaltuwa, jinƙansa, tausayi da rayuwarsa abar koyi. Waƙoƙinsu sun samar da yanayin shauƙi tare da sabunta ƙauna ga Manzon Allah (SAW).

Da misalin ƙarfe 12:27 na rana, an gayyaci Malam Bazallahi Sheikh Nasiru Kabara domin ya gabatar da bayani kan Mu’amalatu Ma’aiki wa Ṣaḥabatihi—wato kyakkyawar alaƙa da mu’amala tsakanin da Manzon Allah Muhammad (SAW) da Sahabbansa masu daraja.

Ya bayyana cewa alaƙar da ke tsakanin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa ta ginu ne a kan zurfin ƙauna da girmama juna, sadaukarwa da cikakkiyar biyayya. Alaƙarsu ba kawai ta shugaba da mabiyansa ba ce; wata kyakkyawar alaƙa ce da aka gina bisa imani, aminci, tausayi, amana da kuma haɗin kai wajen tabbatar da addinin Musulunci.

Ya kuma jaddada cewa Sahabbai sun kasance suna matuƙar ƙaunar Annabi (SAW), suna girmama shiriyarsa, suna tsayawa tare da shi a kowane lokuta koda kuwa akwai ƙalubale, kuma sun kasance a koyaushe a shirye don sadaukarwa saboda Allah da Manzonsa. Ya kawo misali da yaƙin Uhudu a matsayin ɗaya daga cikin manyan misalan gwajin sadaukarwa da Annabi (SAW) da Sahabbansa suka fuskanta tare da shi.

Malam ya bayyana cewa Annabi (SAW) ya kasance yana mu’amala da Sahabbansa cikin nuna ƙauna da soyayya da kuma tsantsar son su da alheri da mutunci da tausayi da fahimta, kuma a haka ya tarbiyyantar da su har suka zama al’umma guda da imani da ‘yan’uwantaka suka haɗa su.

Sheik Bazallahi Sheikh Nasiru Kabara ya ƙara bayyana cewa mu’amalar Annabi (SAW) da Sahabbansa ta samar da wani abin koyi na har abada wajen shugabanci mai cike da tausayi, zumunci mai ɗauke da mutunci, da kuma aminci da aka gina bisa imani. Alaƙar da ke tsakanin Annabi (SAW) da Sahabbansa tana nan a matsayin babban darasi na ƙaunar juna da girmamawa da sadaukarwa da biyayya.

Yayin da zaman musamman na Maulidin Annabi (SAW) ya kusa ƙarewa cikin farin ciki da annashuwa a cikin sa’o’in yamma, malamai da dama sun hau dandamali domin gabatar da nasihohi da wa’azuzzuka masu ilmantarwa ga mambobin Triple R Kannywood Renewed Hope da ɗimbin baƙi da suka halarci taron.

Malamai sun yi kira ga mahalarta da su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW), tare da yin amfani da tasirinsu a masana’antar Kannywood wajen inganta haɗin kai da nuna ladabi da tarbiyya da kyawawan ɗabi’u a cikin sana’arsu da kuma al’umma.

An rufe taron ne da gabatar da addu’o’i da fatan alheri, tare da yabawa mahalarta da masu shirya taron, a wani yanayi mai cike da soyayya da sabunta ƙauna ga Manzon Allah (SAW).

By Babaji

Leave a Reply