Taron G100 ya fuskanci ƙalubale yayin da Atiku, Obi, Kwankwaso da Amaechi ba su halarta ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban taron farko na ’yan adawa da aka shirya domin samar da haɗin kai gabanin babban zaɓen 2027 ya fuskanci ƙalubale a ranar Litinin a Abuja, bayan wasu fitattun jagororin adawa sun kasa halartar taron.

An shirya taron ne ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar matsin lamba ta G100 tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ’Yan Tsiraru ta Majalisar Wakilai, a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.

Manufar taron ita ce samar da tsarin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun adawa domin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya, tare da tattauna batun kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta shekaru huɗu.

Sai dai rashin halartar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi; Sanata Rabiu Musa Kwankwaso; da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya jefa inuwa kan taron.

Ba a bayyana wani dalili a hukumance daga wakilan jam’iyyunsu kan rashin halartar fitattun ’yan siyasar ba.

Duk da haka, wasu jam’iyyun adawa sun samu wakilci a taron, ciki har da Social Democratic Party (SDP), Peoples Redemption Party (PRP), Democratic Leadership Alliance (DLA) da Allied Peoples Movement (APM).

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP, Prince Adewole Adebayo, tare da mataimakinsa, Dakta Usman Bugaje; ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP, Donald Duke; ɗan takarar DLA, Ambasada Moses Olusola; da ɗan takarar mataimakin Shugaban ƙasa na APM, Lawal Daura.

A jawabinsa na buɗe taron, Darakta Janar na G100 kuma tsohon Darakta Janar na Progressive Governors’ Forum, Salihu Mohammed Lukman, ya yi gargaɗin cewa ci gaba da rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa na iya bai wa jam’iyyar APC mai mulki damar samun nasara a zaɓen 2027.

Lukman ya ce jam’iyyun adawa sun sha shiga zaɓukan shugaban ƙasa daban-daban, lamarin da ke haifar da rarrabuwar ƙuri’unsu tare da bai wa jam’iyya mai mulki damar cin gajiyar hakan.

Ya buƙaci jam’iyyun da su fara mayar da hankali wajen tsara ƙa’idojin haɗin gwiwa kafin a fara tattauna sunayen ɗaiɗaikun ’yan takara.

Ya ba da shawarar kafa Kwamitin Jagoranci na Tsakiya, da wasu ƙungiyoyin aiki guda biyar, tare da samar da yarjejeniya mai ɗaurewa ta shekaru huɗu mai taken “National Covenant for Democratic Renewal.”

Shi ma Shugaban ’Yan Tsiraru na Majalisar Wakilai, Frederick Agbedi, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su haɗa kai tare da fifita matsalolin da ’yan Nijeriya ke fuskanta a kan muradun siyasa na ɗaiɗaikun mutane.

“Nijeriya tana cikin raɗaɗi. Nijeriya tana cikin wahala. Idan muka haɗa kai, za mu iya maimaita abin da APC ta yi a shekarar 2015. A wajenmu, babu batun fifita wani ɗan takara,” inji shi.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC mai kula da yankin Kudu maso Kudu, Usani Uguru Usani, wanda ya jagoranci tawagar jam’iyyarsa, ya buƙaci mahalarta taron da su yi aiki tare domin kayar da APC a zaɓen 2027.

Shi kuma Shugaban Jam’iyyar PRP na ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce babu wata jam’iyyar adawa guda ɗaya da za ta iya kayar da APC ita kaɗai, yana mai bayyana wannan yunƙurin haɗin gwiwa a matsayin wata babbar alamar fata ga ’yan Nijeriya.

Tsohon Gwamnan Jihar Neja kuma mamba a Kwamitin Amintattu na PDP, Babangida Aliyu, ya buƙaci mahalarta taron da su tabbatar da ci gaba da wannan tsari.

Ya koka kan yadda muradun kashin kai da na kuɗi suka fi rinjayar muradun ƙasa, yana mai ba masu shirya taron shawarar faɗaɗa tattaunawar zuwa matakin jihohi da ƙananan hukumomi domin tabbatar da shigar mambobin jam’iyyu daga matakin ƙasa.

A saƙon fatan alheri, Shugaban SDP na ƙasa, Farfesa Sadiƙ Umar Gombe, ya ce halin da ƙasar ke ciki na buƙatar gaggawar ceto ta ƙasa, yana mai cewa ’yan takarar jam’iyyun adawa baki ɗaya sun samu fiye da kashi biyu bisa uku na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Duk da rashin halartar wasu daga cikin fitattun ’yan adawa, jam’iyyun da suka halarci taron sun amince da fara tsarin tattaunawa mai tsari domin samar da haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027.

An bayyana wannan matsaya ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da kakakin ƙungiyar ’Yan Tsiraru ta Majalisar Wakilai, Hon. Afam Victor Ogene, ya karanta bayan shugabannin ƙasa da manyan jagororin jam’iyyun shida da suka halarci taron sun sanya hannu.

Jam’iyyun sun amince da kafa wasu hukumomin haɗin gwiwa guda uku, waɗanda suka haɗa da Kwamitin Jagoranci na Tsakiya wanda zai zama babban mai yanke hukunci kan harkokin siyasa; Kwamitin Yaɗa Labarai da Sadarwa domin daidaita saƙonnin haɗin gwiwa; da Kwamitin Shari’a domin tsara takardun doka da na kundin tsarin mulki da za su jagoranci haɗin gwiwar.

Haka kuma, an kafa ƙungiyoyin aiki guda biyar da aka bai wa wa’adin kwanaki 30 domin tsara takardun manufofi.

Abubuwan da za su mayar da hankali a kansu sun haɗa da National Covenant for Democratic Renewal, Yarjejeniyar Mulkin Riƙon ƙwarya na Zango ɗaya, Tsarin Gyaran ƙasa, Tsarin Haɗin Kan Jam’iyyun Adawa da kuma taswirar samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya.

Ogene ya ce jam’iyyun sun yanke shawarar wuce muradun siyasa na kashin kai tare da haɗa kai domin magance matsalolin rashin tsaro, tsadar rayuwa da rashin aikin yi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa G100 za ta ci gaba da zama mai sauƙaƙa wannan tsari kuma mai sa ido, ba tare da ƙwace ikon jam’iyyun siyasa ba.

Ana sa ran jam’iyyun da suka halarci taron za su sake haɗuwa a wani taro na gaba domin duba tare da amincewa da tsare-tsaren da ƙungiyoyin aikin za su gabatar.

By ukarofi