Daga AISHA ASAS
Wani iftila’i ya rutsa da fitaccen mawakin Amurka, Lionel Richie, jim kaɗan bayan kammala wani wasan kwaikwayo da ya gudanar a birnin St. Louis, lamarin da ya yi sanadin garzaya da shi asibiti domin duba lafiyarsa.
Mawaƙin mai shekaru 77 ya kammala wasan ne a filin Muny da ke Forest Park, St. Louis, amma bayan saukarsa daga dandamalin, sai ya zube a kasa lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti inda likitoci suka fara duba halin da yake ciki.
Rahotanni sun ce Richie yana ƙarƙashin kulawar likitoci, yayin da ake gudanar da gwaje-gwaje domin gano abin da ya haddasa matsalar. Sai dai har zuwa lokacin da rahotannin suka fito, ba a bayyana wata takamaiman cuta da aka tabbatar tana damun mawakin ba.
Lamarin ya jawo hankalin masoyan mawakin a sassa daban-daban na duniya, musamman ganin cewa Richie na cikin mawakan da suka shafe shekaru da dama suna ci gaba da fitowa kan dandamali suna gudanar da wasannin kiɗe-kiɗe.
Abin da ya ƙara sanya lamarin ɗaukar hankali shi ne yadda mawaƙin ya samu kansa cikin wannan hali ne bayan kammala wasan, bayan ya yi sallama da masoyansa ya sauko.
Yanzu dai hankalin masoyansa ya koma kan halin da yake ciki, yayin da ake jiran karin bayani daga ɓangarensa ko daga likitocin da ke kula da lafiyarsa.
