Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin man fetur ya ƙara tashi a sassan Nijeriya, inda litar man ta kai tsakanin N1,310 zuwa N1,400 a wasu wurare, yayin da Matatar Mai ta Dangote ta kare matakin da ta ɗauka na ci gaba da ƙara farashin man duk da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Kamfanin ya danganta ƙarin farashin da tsadar ɗanyen man da ya riga ya saya tun farko, da kuma tsawon lokacin da ake ɗauka wajen kammala cinikin ɗanyen man, jigilar shi zuwa Nijeriya da kuma sauke shi a matatar.
A halin yanzu, ana sayar da litar fetur kan kusan N1,310 a Legas da Ogun, yayin da farashin ya kai N1,350 ko fiye a jihohin Arewa da sauran wuraren da ke da nisa da matatar.
Sabon ƙarin farashin ya biyo bayan shawarar Matatar Dangote na ƙara farashin fetur da take bayarwa daga bakin matatar, wato gantry price, da N65 kan kowace lita, daga N1,200 zuwa N1,265.
ƙarin, wanda ya fara aiki ranar 29 ga Agusta, shi ne karo na uku da matatar ta ƙara farashin fetur cikin kwanaki takwas. Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ke raguwa, duk da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.
Sai dai wani babban jami’in Matatar Dangote, wanda ya yi magana da manema labarai ba tare da bayyana sunansa ba saboda ba shi da izinin yin magana a bainar jama’a, ya ce farashin ɗanyen mai da ake gani a kasuwar duniya a yau ba shi ne kawai abin da ake amfani da shi wajen ƙayyade farashin fetur da ake samarwa daga ɗanyen man da matatar ta riga ta saya ba.
Jami’in ya bayyana cewa akwai tazara mai yawa tsakanin lokacin da matatar ta sayi ɗanyen mai da lokacin da kayan suka iso matatar domin tace su. Ya ce kafin ɗanyen mai ya iso matatar, akwai matakai da dama da suka haɗa da kammala ciniki, samun lokacin da jirgin ruwa zai ɗora kayan, hayar jirgin, ɗora ɗanyen man, tafiyar jirgin zuwa Nijeriya da kuma samun gurbin sauke kayan a tashar jiragen ruwa.
“Idan kana son sayen ɗanyen mai da farashin yau, yaushe kake ganin za ka kammala cinikin? Yaushe za ka samu lokacin ɗora shi? Yaushe za ka iya hayar jirgi kuma ku sanya hannu kan yarjejeniyar hayar jirgin?” inji jami’in.
Ya kuma yi tambaya kan yadda za a yi da ɗimbin ɗanyen man da matatar ta saya a baya lokacin da farashinsa ya fi na yanzu tsada kuma aka adana shi a tankuna. Ya ce waɗannan abubuwa ne ke tasiri wajen sauya farashin fetur, ba wai sauyin farashin ɗanyen mai na yau da kullum kai tsaye ba.
Matatar Dangote ta fara ƙara farashin fetur daga N1,165 zuwa N1,185 kan kowace lita a ranar 21 ga Agusta. Bayan kwanaki biyar, ta sake ƙara N15, inda farashin ya koma N1,200 daga ranar 26 ga Agusta. A ranar Asabar, 29 ga Agusta, ta sanar da ƙarin N65, wanda ya kai farashin zuwa N1,265 kan kowace lita.
Hakan ya sa matatar ta ƙara farashin fetur da jimillar N100 cikin kwanaki takwas, wato ƙarin kusan kashi 8.6 cikin 100. Haka kuma, farashin fetur da matatar ke sayarwa ga masu ɗaukar kaya ta hanyar ruwa ya tashi daga N1,582,380 zuwa N1,669,545 kan kowace metric ton.
A sanarwar sauya farashin, matatar ta umarci kwastomominta da su mayar da tsofaffin Izinin Karɓar Kaya (ATCs) domin sake farashi, kafin a ba su sabbin kwangiloli da za su ba su damar ci gaba da ɗaukar man.
Tasirin sabon ƙarin ya fara bayyana a kasuwar sayar da man fetur, inda ake sayar da lita kan kusan N1,310 a Legas da Ogun, yayin da a wasu sassan Arewa da wuraren da ke da nisa da matatar farashin ya kai N1,350 ko fiye.
Rahotanni sun nuna cewa a wasu wuraren farashin ya kusa kaiwa N1,400 kan kowace lita. Bambancin farashin daga wuri zuwa wuri na da alaƙa da kuɗin jigilar fetur daga matatar da ke bakin teku da wuraren ajiya zuwa garuruwan da ke da nisa, tare da ƙarin kuɗaɗen sufuri da rarrabawa. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa Matatar Dangote ke shirin faɗaɗa tsarin rarraba fetur kyauta zuwa sassan ƙasar.
