Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya karɓi baƙuncin Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (wato Dubai) a Legas, Salem Aljaberi, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa alaƙar Nijeriya da UAE tare da bunƙasa damar zuba jari da haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Rabiu ya bayyana farin cikinsa da karɓar babban jami’in diflomasiyyar UAE, yana mai yabawa ƙoƙarinsa wajen ƙara ɗaure dangantaka tsakanin Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
“Babban abin alfahari ne a gare ni na karɓi Mai Girma Salem Aljaberi, Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Legas, a ofishina a yau,” inji Rabiu.
Shugaban BUA ya ce ganawar ta ba su damar musayar ra’ayoyi kan damar da ke gabansu, yana mai bayyana fatansa na ganin alaƙar Nijeriya da UAE ta ƙara ƙarfi tare da samar da alfanu na zahiri ga ƙasashen biyu da al’ummarsu.
“Na ji daɗin musayar ra’ayoyi kan damar da ke gabansu. Ina fatan dangantakar Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta ci gaba da ƙarfafa, tare da samar da gagarumar fa’ida ga ƙasashen biyu,” inji shi.
Rabiu ya kuma gode wa Aljaberi bisa ziyarar da ya kai masa da kuma abin da ya bayyana a matsayin “ci gaba da ƙoƙarin gina gadar zumunci” tsakanin Nijeriya da UAE.
Ganawar na da muhimmanci musamman ganin yadda Rukunin Kamfanonin BUA ke ƙara faɗaɗa harkokinsa a muhimman ɓangarorin tattalin arzikin Nijeriya. Rabiu ne ya kafa BUA Group, wani babban rukuni na kamfanoni da ke da manyan jarin kasuwanci a fannonin siminti, samar da abinci, masana’antu, noma da gine-ginen ababen more rayuwa.
Kamfanonin rukunin na samar da guraben ayyukan yi ga ’yan Nijeriya, tare da tallafa wa ɗimbin harkokin kasuwanci da masana’antun cikin gida da ke cikin jerin masu samar da kayayyaki da ayyuka ga kamfanonin.
Haka kuma, BUA Cement da BUA Foods, waɗanda ke cikin kamfanonin rukunin da ake sayar da hannayensu a kasuwar hada-hadar hannayen jari, sun ci gaba da samun manyan kuɗaɗen shiga da riba, abin da ke nuna irin gudunmawar da ƙungiyar ke bayarwa ga ayyukan masana’antu da kuma samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Sai dai batun ganawar bai tsaya kan harkokin kasuwancin BUA kaɗai ba. A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwar Afirka, Rabiu ya nuna cewa akwai babbar dama wajen ƙara faɗaɗa dangantakar tattalin arziki tsakanin Nujeriya da UAE, musamman ta fuskar zuba jari da haɗin gwiwar ’yan kasuwa. Ya ce yana fatan dangantakar ƙasashen biyu za ta ci gaba da ƙarfi, tare da sauya wannan kyakkyawar alaka zuwa alfanu da za a iya gani kai tsaye ga al’ummomin Nijeriya da UAE da kuma tattalin arzikinsu.
