Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasa ta ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara dawo da amincewar ’yan kasuwa da masu zuba jari ga yanayin kasuwanci a Nijeriya, tare da samar da sabbin damammaki ga ’yan kasuwa su bunƙasa.
Mataimakiyar Fasaha kan Shirye-shiryen Ci Gaban Yankuna a Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa, Dakta Nafia Abdullahi, ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi yayin ƙaddamar da sabon shagon kasuwanci na Makib Estilo da aka buɗe a Central Area, Abuja. Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta ƙaddamar da cibiyar kasuwancin.
A wajen bikin, ministar ta ce kasuwanci na samun ci gaba cikin sauri saboda irin tallafin da gwamnatin Tinubu ke bai wa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa ta hanyar asusun tallafi na musamman, rancen kuɗi masu ƙarancin ruwa, da kuma shirye-shiryen yi wa ’yan kasuwa rajista kyauta.
Yayin da take goyon bayan bayanin ministar, Dakta Abdullahi ta ce yadda kamfanin ya bunƙasa daga ƙaramin shago zuwa babbar cibiyar kasuwanci mai fannoni daban-daban na daga cikin abubuwan da ke nuna ingantuwar yanayin tattalin arziki a ƙarƙashin shirin Sabunta Fata na Gwamnatin Tarayya. Ta kuma ƙalubalanci ’yan siyasar adawa da ke sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu da su riƙa ziyartar wuraren kasuwanci tare da tattaunawa da ’yan kasuwa da talakawa kafin su yanke hukuncin cewa sauye-sauyen gwamnatin sun ƙara tsananta halin tattalin arziki.
Dakta Abdullahi ta ce ya kamata masu sukar gwamnatin su duba sauye-sauyen cikin adalci, tana mai cewa duk da cewa sauyin tattalin arziki na iya zama mai wahalar karɓa a farkon lokaci, ’yan Nijeriya suna sannu a hankali suna sabawa da sabon yanayin tare da fara fahimtar amfanin da zai iya haifarwa.
“Sauyi ba abu ne mai sauƙin karɓa ba. Mutane ba sa saurin sabawa da sauyi. Ni kaina ba na saurin sabawa da sauyi,” inji ta.
A cewarta, sauye-sauyen na kawo wasu sababbin abubuwa a tsarin tattalin arzikin Nijeriya, amma tasirinsu na ƙara bayyana yayin da ’yan kasuwa da sauran jama’a ke sabawa da sabon tsarin. Ta ce, “Abin da ke faruwa yanzu shi ne ƙasar na shigar da wasu abubuwa da ’yan Nijeriya ba su saba da su ba. Amma a hankali suna fara sabawa da su, suna kuma ganin muhimmancinsu da irin tasirin da suke yi mai kyau ga tattalin arziki.”
Dakta Abdullahi ta ce gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin sun fara rage wasu daga cikin matsalolin da a baya suke addabar ’yan kasuwa, musamman waɗanda suka dogara da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje. Ta ce, ci gaban da aka samu a kasuwar canjin kuɗin waje na daga cikin muhimman abubuwan da suka taimaka wajen dawo da kwarin gwiwar ’yan kasuwa.
Ta bayyana shirin Sabunta Fata na gwamnatin Tinubu a matsayin wani muhimmin tsari da ya kawo sauƙi ga ’yan kasuwa da masu sana’o’i. Ta tuna cewa faɗuwar darajar naira sosai a baya ta ƙara tsadar shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, lamarin da ya sa bunaasa kasuwanci ya zama mai wahala.
“Idan ka kalli dala, kamar yadda ’yar uwata ta ambata tun farko, a baya dala na ci gaba da tashi cikin sauri, wanda hakan ya sa shigo da kaya cikin Nijeriya ke ƙara wahala. Amma bayan an fara aiwatar da gyare-gyaren tattalin arzikin, komai ya fara saukowa. Za ka iya ganin cewa kasuwancin ya samu daidaito,” inji ta.
Dakta Abdullahi ta ce Fatima Abdullahi Bono ce ta kafa Makib Estilo, wanda aka fara kusan shekaru bakwai da suka gabata da sunan Makib Apparels, kafin daga bisani ya faɗaɗa zuwa cibiyar da ke samar da kayayyakin cikin gida, kayan girki, yadudduka da sauran kayayyakin amfanin gida da na rayuwar yau da kullum.
Ta kuma ce sauya sunan kasuwancin zuwa Makib Estilo ya samo asali ne daga buƙatar haɗa fannoni da kayayyakin da kamfanin ke samarwa, da kuma rassansa, ƙarƙashin suna guda. Ta ƙara da cewa hakan zai bai wa abokan ciniki damar samun kayayyaki daban-daban a wuri guda cikin sauƙi.
