Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Alhaji Yusuf Muhammed Argungu (Zarumman Matasan Kabi) ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimakawa ɗalibai yayan talakawa wajen karatu.
Ya yi wannan kiran ne ƙarshe makon nan wajen bikin yaye ɗaliban makarantar PADWO da suka kammala karatu a fannin kiwon lafiya.
Zarumman Matasan ya bayyana cewa yana da kyau waɗanda Allah ya horewa halin taimaka wa da yi ƙoƙari su rinƙa taimakawa yayan talakawa a ɓangaren karatu musamman ga waɗanda ke son yin karatun amma iyayen su ba su da halin kai su makaranta saboda idan kuka ki yin haka to ba shakka wata rana suna iya zame maku barazana ga rayuwa.
Ya ƙara da cewa bayan sun kammala karatu sannan har wa yau ku nemi hanyar nema masu aiki saboda rashin aikin yi shi ma wata babbar matsala ce ga al’umma musamman waɗanda suka yi karatu a fannin kiwon lafiya.
Ya kuma nemi gwamnati da ta ta ƙirƙiro gurabun aiki na dindindin ko kuma su rinƙa ba su aikin riƙon ƙwarya wanda a duk lokacin da za a ɗauki ma’aikata ba sai gwamnati ta wahala ba wajen neman ma’aikata.
Ya kuma yi kira ga ɗaliban da aka yaye da su san fa cewa yanzu sun tashi daga wani mataki zuwa na gaba saboda haka su mayar da hankali su zame wa wannan makarantar jakadu nagari a duk inda suka sami kawunan su.
