Mai hana sallah zai koyar da tufar gargajiya?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Taron ranar zallawa wai zai baje kolin tufafin gargajiya na Hausawa! alhali zallawa hana-sallah da mata masu ƙona gashi ne Hausawa a wajensu. Kuma haka su ka gudanar da majalisin ba wani abu na gargajiya da su ka nuna sai rawar koroso da ko ina ma a Arewa akwai ƙungiyar koroso.

Cikin alamun farko da na ankara da Zallawa ‘yan iƙirarin Hausa Zalla ba Hausawa ba ne kuma kwangila ce ta barandar AIFOB ta sa ka su dinga rigar Hausawa, shi ne yanayin rigunan “T’shirt”, hulunan hana-salla da kuma mata ‘yan gagara masu ƙona gashi ko ƙara gashin doki don burge ‘yan bariki da sauran ‘yan birni. Wannan ma baya ga rashin iya rubutu, ba a ma batun ƙa’idar rubutun Hausa ga tsamin baki na rashin iya furta hatta sunan NIJERIYA da Hausa sai “Nijeiriya” ga kuma zunduma ashar da zagin iya malaman Musulunci da yabawa waɗanda ba Musulmi ba.

A taron da su ka gudanar wai na ranar Hausa marar asali ta kowace fuskar doka da oda da dattijantaka, sun ce za su baje kolin tufafin gargajiya na Hausawa! Yo mutanen da ko karambani su ka yi wajen sa rigar Hausawa sai ka ga rigar ta yi wani dagajaja wanda ya saka rigar ya yi kerere! Kayan sam ba nasu ba ne kuma ba za su taba yi mu su kyau ba. Kai ko hula ɗinkin gargajiya su ka saka sai ka ga KOLOJI-KOLO ta yi dungu ko ta yiwa kan yawa ko ta yi cororo a tsakar ka ga kuma rashin iya kari kamar laimar kwadi.

Duk abun da ka ke iƙirarin za ka yi, to a gan shi a zahiri a jikinka. Hatta hotunan AI da su ke tsarawa na nuna hotunan Gwarawa ne. Ko dabarun nuna hotunansu a masallatan Jumma’a rike da sallaya, za ka ga masallacin can daban su nan ragajab daban Gambal Habaru kenan. In ba kai ba ne kawai ba za ka taɓa zama Sallau ba, sai salati ya nuna a bakinka, ba kurba kamru uwar laifi da tasbihin ashar safiya da maraice ba.

Maza da warwaro mata da wanduna! Haka a ke Hausawa a mahangar Zallawa? Kai ku raba ni da magana, na yi nan da gaggawa.

Mai gayyatar taron ranarsa da sunan hausa ya tabbatar da ranar ba ta da asali daga kowane magabaci. Ba wata kungiya ko mutum ɗaya tilo da ke da hurumin ayyana rana a matsayin ta hausa sai in dubu ta taru!

Mai gayyatar taro da sunan ranar Hausa ya fito da sakamakon bincike na na’urar yanar gizo da ke tabbatar da, ba wata hukuma, masarauta ko jami’a da ta amince da yin hakan. Mutumin nan da bai ma iya rubutun Hausa ba balle ma in ya buɗe baki ya na magana ka san dan haye ne; ya tambayi na’ura ko shin hukumar ilimi da al’adu ta majalisar ɗinkin duniya ta ayyana rana musamman don Hausa. Nan na’ura ta ce sam hukumar wato UNESCO a taƙaice ba ta ayyana ranar ba amma wasu ko wani ne kawai su ka ƙirƙiro hakan daga bara-barar nan 2025.

Shin duk malaman jami’a farfesoshi na harshen Hausa ba su da darajar da za a zauna da su don bita kan wannan muradi don sanin muhimmanci ko akasin haka? Ina Sarakuna, ko ba ko ɗaya ne da Zallawa ke girmamawa? Ina manyan marubata littattafai na harshen Hausa? Ga ma Malam Ibrahim Sheme na nan a yanar gizo. Kai Hausa fa ta wuce sanin waɗannan mutanen da ko a makaranta ba su dau Hausa a matsayin wani darasi mai muhimmanci ba. Duk wanda ya yi musu ya nuna sakamakon jarrabawarsa inda ya zauna a darasin harshen Hausa da makin da ya samu. Duk ‘yan kwangilar AIFOB ne da Midibelawa.

Shin babban farfesa Abdulkadir Dan Gambo na jami’ar Bayero ba ya nan ne da wasu tsiraru za su yi wannan wuce gona da iri na cin fuska ga manya? Shi ya sa fa taron kakaf ba inda a ka kawo batun ADABI ko kwarewar harshe sai rawa, dambe da sauran sharholiya. Kai ba na ganin za a bar wani ya yi wa Hausa wannan hawan ƙawara har ma a gari irin Kano. Ina fatan Kanawa za su fahimci masu kunna wannan sakarci su kuma taka mu su birki nan take da duk wani yunƙurin maimaita irin wannan majalisi. Ba wani mutum tilo da ke da hurumin ayyana rana a madadin miliyoyin Hausawa sai in dubu ta taru; amma za su iya taro na rawa da waka ba wanda ya hana su.

Gwarawan nan sun yi miƙa har sun wuce bargonsu. Zagi da ƙirƙirar ƙarya ne sana’arsu dare da rana don dama masu zaman kashe wando ne gabanin samun wannan aiki na wargaza Arewa. Sai a tabaron Bagware ne zai ɗauka akwai wani tasiri na ranar Hausa, harshen da kullum ma ranarsa ce. Sam mutanen nan maƙiya Hausa da Hausawa ne don sun ɗinka rigar ta karya don yi wa Hausawa shigo-shigo ba zurfi. A taka mu su birki. Tsaro ga al’ummar Arewa maso yamma duk ba damuwar Zallawa ba ne don yanzu haushi ma ya turnuƙe su da fitinar ke raguwa.

Wallahi ban da waɗanda su ka wur-wurga karin magana da sunan ranar Hausa, sam ban ga wata riba da ranar ta cimma ba don ‘yan bazata sun yi kaka-gida. Da an kawo maganar ƙabilanci sai ka ji zallawa sun ɓarke da tafi raf-raf-raf kamar tafin hannunsu na katako ne

Da alamu akwai waɗanda ko don siyasa ko kawai ganin shafuka barkatai a yanar gizo na Zallawa, ya sa su ka ɗauka ko mutanen nan na da wani amfani ko tasiri har za ka ga wanda ba kayi tsammani ba wai ya na taya al’ummar Hausawa ranar Hausa! Yaushe al’ummar Hausawa su ka zauna su ka ayyana rana don Hausa? Kai ruɗewa da muradun siyasa ba kyau Wallahi.

Na ga wanda ko waɗanda su ka yi faifan bidiyo wai su na taya Hausawa murnar ranar Hausa. Yaushe miliyoyin Hausawa su ka ware irin wannan rana? Kai wani har tabarau zai makala a idonsa amma in ya tabka wata kwaba sai ka ga tamkar ko ajin A B C D bai taba shiga ba.

Batun za a nuna al’adun Hausawa daga taron masu sanya hula hana-sallah, waƙa ko rawa da dambe duk ai ba wani tasiri da hakan ya yi duk da kawai wasu ne ke magana har da jawo aya ko hadisi a tsakanin mutanen da ke tutiyar KABILA TA FI ADDINI da masu cewa AN DAINA YAUDARARSU DA ADDINI kazalika da masu cewa su na da kirista a cikinsu amma ko aya daya tak a Baibul ba wanda ya ja don tsananin makircin mannewa a jikin Musulunci don yaudarar al’ummar Hausawa na gaskiya.

Kai taron mai wasa da kura ko maciji a gefen kasuwa ya fi wannan taro na waɗanda ke boye kansu a soshiyal midiya su na zagin malaman musulunci su ka yi. Haƙiƙa ba wani abu na sisin kobo da Hausawa su ka amfana da shi a taron sai farafaganda da ɓarkewa da tafi raf-raf-raf-raf daga waɗanda da alamu ba su saba zuwa taruka ba don haka su ka birkice.

Shin wane dattijo ne ko wane masani ne na gaske ya halarci taron Zallawa kuma menene abu daya tak da ya shafi bunkasa harshen Hausa da taron ya cimma? Tabbas Zallawa da alamu sun sauya wasu abubuwan da su ka tsara yin dabdala a kai don haska makircinsu da tocila mai batur 18…War war ware Gaja.

Duk wanda ya halarci taron zallawa da sunan ranar Hausa to haƙiƙa ya cancanci a zaunar da shi a ba shi ruwan sanyi in ya huce sai a yi ma sa nasiha mai ratsa zuciya ko a dace ya gane in ya na da sauran rabo.

ina kira ga gwamnatin kano ta takawa zallawa birki don cin mutuncin Hausawan ya isa hakanan

Ni na ma wuce batun ranar Zallawa da bagayen wai ranar Hausa, sai na ga har yanzu wasu na zakewa ko da gangan ko jahilci kan fahimtar wannan taro fakewa ne da guzuma don a harbi karsana. Duk masu hayaniyar nan a soshiyal midiya ba su da alaka da Hausa sai zangar wannan muguwar kwangilar wargaza Arewa ta sanya rigar karya ta Hausa wato logar kara da fatar akuya.

Wai asalin taron shi ne wasu Zallallu sun yi taro ko a Tiktok ko wata kafar soshiyal midiya sai su ka ga me zai hana su juya wannan zuwa taron ranar Hausa! Ka ji sai ka ce a Tiktok a ka ƙirƙiri Hausa. Don rashin kunya a rasa ma inda za a yi wannan magana sai a tsirara a yanar gizo. Duk da ma ba mamaki don masu shirya abun yawanci ‘yan ƙananan yara ne da ba su san ma inda duniya ta dosa ba, duk inda guguwa ta kada sai su garzaya can kamar taron ledoji a juji idan guguwa ta kada sai ta watsa su kan jinka da salga ba zabi.

KAMMALAWA

Ina nanatawa cewa masoya manyan harsuna kan yi taruka ne kan ADABI na harshe kamar ranar Turanci inda a ke yi don girmama Shehun Shehunai na adabin Turanci wato William Shakespeare SHEHU GIRGIZA MASHI. Duk wanda ya karanta ADABI na Turanci ya san waye Shehu Gizgiza Mashi 1564-1616. A kan yi hakan ranar 23 ga Afrilu. Ranar Larabci ma 18 ga Disamba don ADABI da duba ayyukan Gangaran a harshen ka fi Gwani SIBAWAIHI. Majalisar ɗinkin Duniya ta dau Larabci a matsayin daya daga harsuna 6 da a ke amfani da su a tarukan majalisar a 1973 kuma an yi hakan 18 ga Disamba.

Duk irin waɗannan taruka ba rawa ba waƙa ba dambe ba ƙabilanci ba AIFOB da Midil bel; a kan duba tsantsar ilimin ADABI ne don masu ilimin harshe ke taron kuma ba lallai ma ‘yan harshen ba. Shi ya sa a kiyayi abun da tantiran jahilai da ‘yan arufta su ka tsara don cimma burin makiya Lardin Arewa.

Ina kira ga gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su ɗau matakan dakatar da duk wani Bazalle daga yin irin wannan taro don akwai boyayyiyar manufa fiye da abun da a ke yayatawa na fili. A takawa Zallawa birki don wani lokacin mai karambani sai an zungure ma sa hanci ya san akwai hukuma a kasa.

By ukarofi

Leave a Reply