An gurfanar da ɗan Katsina kan zargin cin amanar ƙasa bisa cire allon tallar Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An tsare wani mazaunin Jihar Katsina, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nesta, tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin aikata laifin cin amanar ƙasa, bayan zargin cewa ya lalata allunan tallan siyasa da ke ɗauke da hoton Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Da farko ’yan sanda a Katsina sun gayyaci Sanda domin yi masa tambayoyi, kafin daga bisani su tsare shi bisa zargin cewa ya cire allunan tallan Shugaba Tinubu tare da kutse cikin Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, inda aka zarge shi da kwashe kuɗi har Naira miliyan 35.

Sai dai Sanda ya musanta zarge-zargen, ciki har da zargin lalata allunan tallan Tinubu da kuma kutsawa cikin sakatariyar APC domin satar kuɗin. Ya bayyana zarge-zargen da cewa ba su da tushe.

Daga baya, an mayar da Sanda zuwa Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da ke Abuja, inda wata Kotun Majistare da ke zama a Jiwa, a Babban Birnin Tarayya Abuja, ta bayar da umarnin tsare shi bisa wasu tuhume-tuhume da suka haɗa da laifin cin amanar ƙasa.

’Yan sanda sun nemi kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Sanda na tsawon makonni biyu domin ba su damar kammala bincikensu. Sai dai a ranar Talata, lokacin da lauyoyinsa suka bayyana a gaban kotu domin neman a bayar da belinsa, ’yan sanda su ma suka gabatar da wata buƙata ta ƙarin makonni biyu domin kammala binciken. Alƙalin Majistare, Huzaifa Macchudo, ya ɗage yanke hukunci kan buƙatar belin.

Lauyoyin Sanda sun ce dage yanke hukuncin na iya bai wa ’yan sanda damar neman ƙarin lokacin tsare shi, yayin da yake ci gaba da kasancewa a hannunsu.

Wata majiya da ke da masaniya kan shari’ar ta tabbatar da cewa an gurfanar da Sanda a ranar Talata. Majiyar ta kuma ce an ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga Satumba domin yanke hukunci kan buƙatar belin da lauyan Aminu ya shigar.

A halin da ake ciki, masana harkokin shari’a sun nuna damuwa kan tuhume-tuhumen cin amanar ƙasa da aka ɗora wa Sanda. Wani lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Hameed Ajibola Jimoh, ya bayyana mamakinsa kan yadda cire allon tallan siyasa zai kai ga tuhumar mutum da laifin cin amanar ƙasa. “Abin mamaki ne a ce cire allon talla zai zama cin amanar ƙasa,” inji shi.

Ya ce doka tana da takamaiman ma’anar laifin cin amanar ƙasa da kuma manyan laifuka, yayin da cire allon tallan siyasa ya fi karkata ga batun siyasa. Jimoh ya ce, zarge-zargen na iya haifar da wasu batutuwan shari’a gwargwadon yanayin abin da ya faru, amma ya nuna shakku kan yadda ake danganta abin da ake zargin Sanda ya aikata da laifin cin amanar ƙasa.

“Ba ya cikin abin da na sani cewa irin wannan abu ya kai matsayin cin amanar ƙasa, sai dai idan aka duba sashe na dokar da aka tuhume shi a ƙarƙashinsa da kuma abin da dokar ta tanada,” inji shi.

Shi ma wani lauya mai zaman kansa da ke Abuja, Barrister Abdurrahman Salis, ya bayyana tuhumar da ake yi wa Sanda da cewa “abin mamaki” ne, yana mai cewa zargin cire allon tallan Shugaba Bola Tinubu, a yadda yake a fili, bai cika ma’anar laifin cin amanar ƙasa ba.

“Abin mamaki ne. Ba lauya kaɗai zai yi mamakin ganin irin wannan tuhuma ba, har ɗalibin shari’a ma zai yi mamaki idan ya ga ana tuhume mutum da irin wannan laifi saboda zargin cire allon tallan Shugaban Ƙasa a Jihar Katsina,” Salis ya shaida wa manema labarai.

Ya bayyana cewa, cin amanar ƙasa da babban laifin cin amanar ƙasa laifuka ne daban-daban a ƙarƙashin dokokin Nijeriya, kuma suna da alaƙa da manyan ayyuka fiye da zargin lalata allon talla.

“ƙarƙashin dokokinmu, domin wani abu ya zama laifi, dole ne doka ta bayyana shi a matsayin laifi. Dole ne doka ta fayyace abubuwan da suka ƙunshi laifin, sannan ta tanadi hukuncin da ya dace da shi,” inji shi.

A cewarsa, laifin cin amanar ƙasa na iya haɗawa da yunƙurin cire Shugaban ƙasa ko gwamna daga muaminsa ta hanyar da ba ta dace da kundin tsarin mulki ba, yunƙurin yaƙi da Nijeriya, ko kuma hannu wajen tayar da zaune tsaye da nufin kai wa ƙasar hari da makamai.

“ƙarƙashin tanadin dokar cin amanar ƙasa da muke magana a kai, babu inda aka bayyana cewa cire allon tallan Shugaban ƙasa laifi ne na cin amanar ƙasa,” inji Salis.

Ya ƙara da cewa, idan aka yi nazari sosai, cire allon tallan Shugaban ƙasa bai cika sharuddan da dokokin Nijeriya suka gindaya na laifin cin amanar ƙasa ba. Sai dai Salis ya ce gwargwadon bayanan da bincike zai gano, abin da ake zargin Sanda ya aikata na iya zama wani laifi daban, amma hakan ba ya nufin laifin cin amanar ƙasa ne.

Lamarin Sanda ya fito ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin zafafa rikicin siyasa a cikin reshen Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Rahotanni sun ce rikicin ya fara ɗaukar sabon salo ne bayan lalata wasu allunan tallan siyasa da ke ɗauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Masari, a sassan Jihar Katsina.

Lamarin ya jawo hankalin ƙasa baki ɗaya bayan rahotannin da suka ce an gayyaci wasu jami’an tsaro biyu da ke aiki tare da Gwamnan Jihar Katsina, Umar Dikko Radda, zuwa Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da ke Abuja domin yi musu tambayoyi kan zargin lalata allunan tallan. Shi ma Sanda ’yan sanda sun gayyace shi tare da tsare shi bisa zargin cewa yana da hannu wajen cire allunan.

Abin da ya ƙara ɗaukar hankalin jama’a shi ne yadda Sanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙungiyar Dikko/Tinubu ɓanguard a Jihar Katsina, wato ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan Shugaba Tinubu. A cewarsa, ba shi da dalilin lalata kayan tallan wani shugaban ƙasa da kuma harkar siyasar da yake iƙirarin goyon baya.

By ukarofi

Leave a Reply