Shaye-shaye da illolinsu ga matasa, lafiya da zamantakewa

Spread the love

Daga  DR. BILKISU YUSUF ALI

Ci gaba daga makon da ya gabata.

Kamar yadda muka faro a makon da ya gabata, shaye-shaye na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al’ummomi da dama a duniya, musamman matasa. Matsalar tana shafar lafiyar jiki da ta kwakwalwa da ilimi da tattalin arziki da tsaro da zamantakewar al’umma. Wannan rubutu ta yi  nazari kan ma’anar shaye-shaye da nau’o’insu, abubuwan da ke jawo matasa shiga shaye-shaye, illolinsu ga lafiyar mutum da zamantakewa, tare da hanyoyin kariya da magance matsalar. Bincike ya nuna cewa haɗin gwiwar iyaye da malamai da shugabannin addini, gwamnati da al’umma yana da muhimmanci wajen rage wannan matsala.

Gabatarwa

Matasa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Idan aka ba su ingantacciyar tarbiyya, ilimi da lafiya, za su zama jagororin gobe. Amma idan suka fada cikin shaye-shaye, hakan na iya lalata rayuwarsu da makomarsu. A yau, shaye-shaye sun zama babban ƙalubale a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya. Matsalar tana haddasa ƙaruwar laifuka da rashin tsaro da rushewar iyalai da rashin aikin yi da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Illolin Shaye-shaye Ga Lafiya

Shaye-shaye ba iya tarbiyya da zamantakewa yake lalatawa ba , shaye-shaye yana lalata  kwakwalwa ya kassara lafiyar jiki da jirkita tunani. 

Shaye-shaye na iya rage ƙwaƙwalwa da ikon yanke shawara

Wanda yake tu’ammali da kayan maye zai zama zai zamana ba shi da kaifin basira da faɗaɗa tunani da yanke hukunci nan take.  

Ciwon zuciya

Wasu miyagun ƙwayoyi na ƙara haɗarin bugun zuciya da hawan jini wanda zai kawo mutuwa ta farat ɗaya. 

Lalacewar hanta

Shan magunguna ba bisa ƙa’ida ba suna lalata hanta. 

Lalacewar ƙoda

Wasu miyagun ƙwayoyi na iya shafar aikin ƙoda.

Matsalolin numfashi

Shan taba da wasu abubuwa na ƙara haɗarin cututtukan huhu.

Matsalolin lafiyar kwakwalwa

Ana iya samun damuwa ko  tashin hankali da  ruɗani ko wasu matsalolin tunani.

Mutuwa

A wasu lokuta, yawan amfani da miyagun ƙwayoyi na iya jawo mutuwa kai tsaye.

Illolin shaye-shaye ga Ilimi

-Rashin zuwa makaranta.

-Faɗuwar jarabawa.

-Korar ɗalibai.

-Rashin mayar da hankali.

-Barin karatu.

Illolin shaye-shaye ga zamantakewa

-Rushewar iyali.

-Rikice-rikicen aure.

-ƙaruwar laifuka.

-Fashi da makami.

-Satar dukiya.

-Rikice-rikicen matasa da daba

-Rashin zaman lafiya.

Illolin shaye-shaye ga tattalin arziki

-Rage yawan ma’aikata masu ƙwarewa.

-Ƙarin kuɗin kula da lafiya.

-Asarar kuɗaɗe saboda laifuka.

-Rage cigaban ƙasa.

Hanyoyin Kare Matasa Daga Shaye-shaye

Iyaye

Haƙƙin iyaye ne su kula da ‘ya’yansu. Addinin musulunci ya koyar da uba ya samarwa ‘ya’yansa uwa ta gari tun kafin a yi auren.  Haka uwa ita ma ya kamata ta zama jajirtacciya kuma tsayayyiya don samarwa yaranta tarbiyya da kula da su. 

Su tattauna da su akai-akai.

Iyaye ya kamata suke tattaunawa kan matsalolin yaransu don shawo bakin matsala tun tana ƙarama. 

Iyaye yana da kyau tun yaransu suna ƙanana suke nusar da su muhimmancin  zama mutumin kirki da son su zama abin koyi.

Malamai

Su ma malamai suna da muhimmiyar rawa da za su taka wurin tarbiyyantar da ɗalibansu  da nusar da su da wayar da kan ɗalibai. Haƙƙin malamai ne su sa ido su gano waɗanda ke cikin haɗari.

Shugabannin Addini

Malamai suna cikin shugabannin al’umma  waɗanda suke tarbiyyar al’umma haka suke saita al’umma a jiki da ruhi . Yana da kyau malamai suke shirya wa’azuzzuka a masallatai da majami’ai  a makarantu da kasuwanni da sauran wuraren haɗuwar al’umma. Yana da kyau a shirya wa’azi kan illolin shaye-shaye. Su ƙarfafa kyawawan ɗabi’u

Gwamnati

Ita ma gwamnati tana da rawar takawa kan shawo kan matsalar shaye-shaye da daƙile ta ta hanyar ƙarfafa dokokin yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Ta samar da ayyukan yi ga matasa.

Ta tallafa wa cibiyoyin kula da masu fama da matsalar.

Kafofin yaɗa labarai

Su ma kafofin yaɗa labarai ba a bar su ba baya ba don suna da rawar takawa a wannan ɓangare. Don haka, yana da kyau su yaɗa saƙonni na wayar da kai  ta kowanne ɓangare .

Su guji tallata halayen da ke ƙarfafa amfani da miyagun ƙwayoyi.

Shawarwari

A ƙara wayar da kan jama’a.

A ƙarfafa tarbiyya a gida da makaranta.

A samar wa matasa ayyukan yi da horo.

A inganta kula da lafiyar kwakwalwa.

A ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da  iyaye da makarantu da ƙungiyoyin addini.

A ƙarfafa aiwatar da dokokin hana safarar miyagun ƙwayoyi.

Kammalawa

Shaye-shaye na daga cikin manyan matsalolin da ke barazana ga lafiyar matasa da ci gaban al’umma. Illolinsu ba su tsaya ga mai amfani kawai ba, har ma suna shafar iyali, tattalin arziki da tsaron ƙasa. Don haka, ya zama wajibi a haɗa kai wajen rigakafi, wayar da kai, gano masu buƙatar taimako da samar da hanyoyin jinya da gyaran hali domin kare makomar matasa da bunƙasa al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply