An ƙara jibge jami’an tsaro a ƙaramar hukumar Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin jami’an tsaro zuwa ƙaramar hukumar Funtuwa a Jihar Katsina, biyo bayan ƙaruwar hare-haren “yan bindiga da aka samu a yankin a ‘yan kwanakin nan.

Wannan mataki da gwamnatin tarayya ta ɗauka wani ɓangare ne na ƙoƙarin maido da zaman lafiya da kare rayukan mazauna yankin a hannun ‘yan ta’adda.

Da yake tabbatar da hakan, wani fitaccen jagoran al’ummar Funtuwa, Alhaji Lawal Abbas Funtua, ya ce ya ɗauki nauyin tallafawa jami’an tsaron da aka turo domin ƙara musu ƙarfin gwiwa.

Da yake magana a Lawal Abbas ya ce wannan tallafin ya ,zama dole garemu taimakawa mazauna yankin da ke neman mafita ta dindin kan matsalar rashin tsaro.

“Gwamnatin Tarayya ta amsa kira ta hanyar tura ƙarin jami’an tsaro zuwa Funtua da sauran ƙananan hukumomi. Dole ne mu tallafa musu da duk abin da muke da ƙarfi a kai domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata,” in ji Abbas.

Ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Funtua da su yi addu’a don samun nasarar jami’an tsaro, tare da ba su cikakken haɗin kai wajen yaƙar ta’addanci da sauran masu aikata laifuka.

“Muna kira ga al’ummar Funtua da su ci gaba da yi wa jami’an tsaronmu addu’a. Tare da basu haɗin kai.

“Abbas ya kuma ya ce zai cigaba da tallafawa jami’an tsaro har sai an samu cikakkiyar zaman lafiya a cikin ƙaramar hukumar Funtua.

Mazauna garin Funtua sun yaba wa Alhaji Lawal Abbas bisa gudummawar da yake bayarwa a harkokin tsaro a yankin.

Al’umma sun bayyana tallafinsa ga jami’an tsaro yazo akan lokaci kuma mai matuƙar muhimmanci, suna mai cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, shugabannin al’umma da ‘yan ƙasa shi ne zai kawo ƙarshen ‘yan bindiga.

“Ƙoƙarinsa ya nuna cewa kare Funtuwa alhakinmu ne baki ɗaya. Muna godiya bisa abin da yake yi domin tsaron mutanenmu,” in ji wani mazaunin garin Funtua Muhammad Garba.

Karamar hukumar Funtua,na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a jihar Katsina, ta sha fama da ƙaruwa hare-haren “yan bindiga a ‘yan makwannin nan, wanda ya haifar da damuwa a tsakanin “yan kasuwa, manoma da mutanen yankin.

Ana sa ran tura ƙarin jami’an zai ƙarfafa sintiri, sa ido da kuma saurin ba da agaji a Funtua da al’ummomin maƙwabtan su.

Shugabannin yankin sun ce suna da kyakkyawan fata cewa tare da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya, jami’an tsaro, da tallafin al’umma, za a samu zaman lafiya mai ɗorewa a Funtua kuma ayyukan tattalin arziki za su dawo kamar yadda suke a ƙaramar hukumar Funtua.

By ukarofi

Leave a Reply