Manoman Nasarawa sun rungumi sabbin dabarun noma daga Sasakawa Afirka

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya

Ƙananan manoma a jihar Nasarawa suna samun ƙarin girbi da abinci mai gina jiki bayan sun fara amfani da sabbin fasahohin noma masu jure sauyin yanayi da kuma iri masu inganci irin na zamani dake ɗauke da sinadaren gina jiki.

Shirin na musamman da ke inganta abincin noma da tallafa wa ƙananan manoman wata ƙungiya da ake kira Sasakawa Africa Association SAA-Nigeria ce ke gudanar ƙarƙashin tallafin gidauniyar NIPPON ta ƙasar Japan.

A lokacin ziyarar manema labarai da aka yi a cikin al’ummomin Tundun Adabu da Angwan Hamidu na ƙaramar hukumar Obi a jihar, manoma sun nuna yadda noma mai sabunta ƙasa da samar da iri a gida da noma da aka mayar da hankali kan abinci mai gina jiki ke taimakawa wajen ƙara yawan amfanin gona da yaƙi da rashin isasshen bitamin a jiki.

Jibril Elayo ɗaya daga cikin manoman ya nuna yadda sabon tsarin dasa iri ɗaya a rami ɗaya da nisan santimita 25 ke kawo sakamako mai kyau. Ya ce ko da yake an jinkirta dasa masara da waken soya saboda rashin daidaiton ruwan sama, amma girbin ya inganta.

“A da ba za ka ga manomi yana dasa iri ɗaya a rami ba saboda tsoron ba zai tsiro ba. Amma yanzu da muka ɗauki wannan tsarin na SAA, mun rage kuɗin siyan iri kuma girbin ya ƙaru,” in ji shi.

Ya kuma bayyana amfanin irin masara ta SAMMAZ 52, wacce ta balaga da wuri kuma tana ɗauke da bitamin A. An dasa ta a ranar 26 ga Yuni, kuma cikin makonni uku za a girbe ta. Irin waɗannan iri suna bawa manomi damar yin noman sau biyu a cikin damina ɗaya.

Shugaban ƙungiyar manoma ta Ayinewoza a garin na Obi, Bashir Ogbole shima ya kwatanta tsohuwar hanyar noma da sabuwar ta SAA. Yace sun karɓi kayan noma a watan Yuli Inda suka fesa maganin ciyawa sannan suka dasa da nisan santimita 75 a ranar 11 ga Agusta tare da amfani da takin NPK da Urea a matakai.

“Akwai babban bambanci. A da ba mu damu da nisa ba kawai mu na dasawa. Amma yanzu kowa na iya ganin gonar da aka kula da ita ta fi kowacce. Idan gwamnati ta taimaka a ɗauki wannan tsari a ko’ina, ƙarancin abinci zai ragu sosai,” in ji shi.

A nasa ɓangaren da yake magana a madadin darakta na ƙungiyar SAA ɗin Dr. Godwin Atser mai kula da juriya da ingancin kan sauyin yanayi yace rawar SAA ita ce haɗa cibiyoyin bincike da manoman da sauyin yanayi ya shafa.

“Muna tattaro iri masu inganci daga cibiyoyin bincike. Iri ne masu jure fari masu saurin balaga da masu yawan amfanin gona da kuma masu jure cututtuka da ƙwari,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa irin waɗannan amfanin gona ba na GMO ba ne sai dai sakamakon kiwo na al’ada. “Wasu iri suna balaga cikin kwanaki 80 maimakon 120. Wannan yana taimakawa manomi ya girbe ko da ruwan sama ya tsaya da wuri.”

Don mayar da ƙarfin ƙasa, SAA na koyar da amfani da biochar da takin gargajiya da haɗa masara da wake. Biochar yana riƙe da ruwa a ƙasa yayin da wake ke saka nitrogen a ƙasa ta hanyar ɗabi’a.

Jami’ar shirin na ɓangaren abinci mai gina jiki Dr. Moshood Sulaiman yace suna ƙoƙarin yaƙi da “yunwar da ba a gani” a ƙauyuka ta hanyar yaɗa masara mai sinadaren bitamin A musamman ga mata masu juna biyu da masu shayarwa da ƙananan yara ƙasa da shekara biyar.

Misis Adama Rabiu wata manomiya mai cin gajiyar shirin ta ce “Tun da Sasakawa ta zo mana, abincin da muke ci ya inganta. Yanzu muna shuka ugu a kusa da gidaje don ƙara wa abincinmu. Wannan ya taimaka mana sosai.”

Don tabbatar da ɗorewa, jami’in noma na kasuwa wato Jonathan Yassah na ƙungiyar Sasakawa Afirka Association din shima yace SAA na kafa cibiyoyin samar da iri da manoman gida za su gudanar tare da yin amfani da iri na asali daga cibiyar.

By ukarofi