
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani masallaci ya kai wa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukwa hari, inda ya sare shi da wani makami a ranar Juma’a jim-kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a yankin Mabera na Jihar Sakkwato.
Rahotanni sun bayyana cewa, cikin hanzari masallata suka ɗauki doka a hannunsu kan wanda aka yi zargin ya ƙaddamar da harin, lamarin da ya kai ga mutuwarsa. Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan Sakkwato, DSP Ahmed Rufa’i ya ce rundunar ta samu labarin aukuwar lamarin.
Ya ce, sun fara bincike kan al’amarin domin gano ainihin yadda ya faru, yana mai cewa za su cigaba da bai wa ‘yan jarida ba’asin halin da ake ciki yayin da aka samu wasu sababbin bayanai.
A baya ne wani jagoran ‘yan daba mai suna Ɗahiru Shehu Maiɓarewa ya yi barazanar kisa kan zargin Shehin malamin da kalaman ɓatanci. An ce ɗan dabar ya bayyana rashin gamsuwa da malamin, wanda hakan ya kai ga zargin barazana ga rayuwarsa. Bayan haka ne aka garzaya da Maiɓarewa zuwa kurkuku.
Makonni kaɗan bayan haka ne aka wallafa wani bidiyo a Soshiyal Mediya da ke nuna Sheikh Lukwa yana tafiya zuwa masallacinsa ɗauke da bindiga a matsayin gargaɗi ga masu yunƙurin neman rayuwarsa.
A yayin haɗa wannan rahoto, an ruwaito cewa Shehin yana karɓar magani a wani asibiti da ke cikin garin Sakkwato. Daga bisani, an yaɗa wani faifan bidiyo da ke nuna malamin yana jawabi bayan karɓar magani kan harin.
