
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar ranar Juma’a aka halaka ‘yan sanda guda huɗu da wasu ƙauyawa takwas a wani hari da ‘yan bindiga suka ƙaddamar a ƙauyen Ayilamo da ke Gundumar Tombo ta Ƙaramar Hukumar Logo a Jihar Benuwai.
Rahotanni sun nuna cewa, mazauna yankin sun ce maharan, waɗanda sun haura mutum 200, sun afka wa garin wanda mafiya yawancin mutanensa manoma ne, ta hanyar Alufu da ke ƙarƙashin Jihar Taraba, sannan suka shiga Ayilamo inda suka buɗe wa mazauna wuta tare da bankwa wa gidaje wuta.
A cewar ‘yan yankin, Ayilamo, wanda ke kan hanyar Abinsi zuwa Tyulen zuwa Anyiin zuwa Wukari, na fama da matsalolin hare-hare, lamarin da ya tilasta wa mutanen wajen kira ga a ƙara adadin jami’an tsaro da ke bai wa yankin kariya.
Wani ɗan wajen mai suna Tyolumun Ugande ya shaida wa ‘yan jarida cewa ‘yan sanda da ke aiki a garin sun yi musayar wuta da maharan, waɗanda suke ɗauke da wasu muggan makamai. Ya bayyana cewa, an shafe tsawon sa’o’i daga daren Alhamis wayewar Juma’a kafin ‘yan ta’addan suka janye, yana mai cewa a washe-gari ne aka gano gawarwakin ‘yan sanda huɗun a cikin juji.
Ya ƙara da cewa, an kuma samu gawa takwas na ‘yan ƙauyen bayan harin, yayin da kuma gidaje da dama suka ƙone ƙurmus.
Rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da saƙo ba kan al’amarin yayin haɗa wannan rahoto duk da cewa ta tabbatar da faruwarsa.
