Hutu: Tinubu ya isa Paris

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Paris na ƙasar Faransa, a matsayin ɓangare na biyu na hutunsa na shekara mai tsawon mako uku da ya je Nahiyar Turai domin gudanarwa.

Hakan ya biyo bayan kammala zamansa ne a Landon ta ƙasar Ingila. Tinubu ya isa babban birnin Faransan ne a ranar Lahadi, 13 ga Satumba, 2026 yayin da wa’adin hutun nasa ya shiga zango na biyu. Sannan, ya samu tarba daga Jakadan Nijeriya a Faransa, Emmanuel Ayodele Oke, a cewar wasu rahotanni da aka fitar kan isar Shugaban.

Wannan shi ne sabon cigaba da aka samu daga hutun Shugaban Nijeriyar, wanda ya fara tun a ranar 30 ga Agusta, 2026 bayan Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da hakan a matsayin hutunsa na shekara.

Fadar ta sanar da cewa, Shugaban zai fara zuwa Landon ne a matsayin birnin da zai yada zango a matsayin ɓangare na hutun nasa, kamar yadda Kakakinsa Bayo Onanuga ya bayyana a sanarwar.

Haka kuma, fadar ta ce Shugaba Tinubu zai dawo Nijeriya ne da zarar ya kammala hutun nasa domin cigaba da gudanar da hada-hadar ƙasa ciki har da shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

By Babaji

Leave a Reply