Matafiya tara sun rasu yayin da wasu suka jikkata bayan ‘yan bindiga sun buɗe wa mota wuta a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimamin mutane 15 ne ‘yan bindiga suka halaka a mabambanta hare-hare a ƙananan hukumomin Jihar Filato uku, ciki har da fasinjoji guda tara da ke kan hanyar zuwa Jos.

Hare-haren sun auku ne a daren Lahadi wayewar Litinin a ƙauyukan Dungusa da ke Jos ta Kudu, Vodni a Mangu da Tahoos a Riyom, lamarin da ya tayar da fargaba acikin mazauna da matafiya a jihar. Mafi muni daga ciki ya auku ne da misalin ƙarfe 9:40 na dare a Dungus, inda wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka buɗe wa wata mota wuta a lokacin da take kan hanyar tafiya zuwa Jos.

Kakakin ƙungiyar Matasan Ƙabilar Berom, Rwang Tengwong ya tabbatar da harin, inda ya ce ɗaya daga cikin waɗanda aka halaka mamba ne na Atisayen Rainbow, wato na wata tawagar tsaro.

Wasu fasinjoji sun samu tsira daga harin ɗauke da raunukan harbin bindiga, waɗanda tuni aka garzaya da su zuwa asibitoci domin ba su magani, saidai wasu sun rasu yayin da suke karɓar magani.

Wani maƙoci kuma malamin ɗaya daga cikin waɗanda iftila’in ya shafa mai suna Lawan Suleiman shi ma ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce ya faru ne a lokacin da aka tsayar da motar a wata madakatar mota. Ya ce, ” Ibrahim ne direban kuma ya kasance ɗalibina. Uku daga ciki ‘yan yankinmu ne nan a Ɓukuru. An kai gawarwakinsu asibiti. Amma iyalansu suna shirin karɓar su domin gudanar da jana’iza.”

A wani labarin kuwa, an halaka wasu mutane shida a wasu hare-hare yayin da aka kashe mutum tara a Jos ta Kudu. Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun farmaki jama’a a yankin Vodni a Gundumar Pushit ta Ƙaramar Hukumar Mangu. An ruwaito cewa, an halaka biyu yayin da aka garzaya da wasu huɗu asibiti sakamakon samun raunuka.

A wani yankin kuma a Ƙaramar Hukumar Riyom an kashe ƙarin wasu mutum biyu a wani hari a ƙauyen Tahoos a lokacin. Waɗannan hare-hare sun yi sanadiyyar rasa jimillar rayuka 15 yayin da aka raunata wasu da dama.

Gwamnatin jihar Filato ko rundunar ‘yan sanda ba su fitar da wani bayani ba kan waɗannan hare-hare yayin haɗa wannan rahoto. Wannan al’amari ya sake jefa al’umma cikin fargaba musamman kan yankuna masu sauƙin fuskantar hare-hare da matafiya acikin dare.

By Babaji

Leave a Reply