Al’umma sun koka yayin da farashin fetur ya kusa N1,500

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da farashin fetur ke cigaba da hauhawa a sassan Nijeriya, al’umma sun nuna damuwa biyo bayan sabunta farashi da Kamfanin Matatar Ɗangote ya yi, inda ya ƙara Naira 85 ga kowace lita yayin da saurin ƙarin farashin mai a matakin ƙasa-da-ƙasa ke cigaba da haifar da matsi.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin man Ɗangote ya ƙara farashin litar ne daga N1,265 zuwa N1,350, wanda ke wakiltar samun kaso 6.7 na ƙarinkuma ya kusanta shi da N1,500 a wasu sassan ƙasar.

Hakan na zuwa ne yayin da aka ga wasu gidajen mai sun ƙara farashin, inda masu ababen hawa suke siyan fetur a tsakanin N1,395 da N1,460 ga kowace lita.

Wannan ya sa al’umma suka shiga damuwa kan yiwuwar cigaba da samun hauhawar farashin ɗanyen mai da sauran kayayyakin makamashi.

Akwai alamu da ke nuna cewa Nijeriya da sauran sassan duniya su cigaba fuskantar hauhawar farashin fetur muddin aka cigaba da yaƙin Amurka da Iran.

Wannan ci-gaba ya zo ne a daidai lokacin da farashin fetur ya riga ya ƙaru a ƙasar bayan ƙare-ƙare na baya a farashin ɗanyen mai da na shigowa ko maye gurbin dangogin fetur.

By Babaji

Leave a Reply